A makon da ya gabata ne, aka fitar da alkaluman kididdigar tattalin arzikin kasar Sin, wanda ke nuna karuwar yawan hajoji da kayayyakin masarufi da Sin ta sayar, zuwa kashi 4.6 cikin 100 kan na shekarar bara, wanda ya karu da kaso 2.1 cikin 100, fiye da na watan da ya gabata. Wannan na kara tabbatar da cewa, alkaluman tattalin arzikin kasar Sin sun inganta, kuma cinikayyar hajojin kasar ta zarce yadda ake zato.
Sanin kowa ne cewa, baya ga wadannan alkaluma, akwai kuma damarmaki na yin kasuwanci da baki daga waje ke sha’awa matuka. Tun daga farkon wannan shekara, farfadowar tattalin arzikin duniya yake fuskantar tafiyar hawainiya, kuma sakamakon durkushewar manufofi a manyan kasashe masu karfin tattalin arziki ya fito fili.
Amma abin farin ciki shi ne, tattalin arzikin kasar Sin ya jure matsin lamba, ya kuma ci gaba da farfadowa, kuma yana ci gaba da zama muhimmin injin na ci gaban tattalin arzikin duniya. Lamarin dake kara baiwa ’yan kasuwa daga sassan duniya karfin gwiwa da sha’awar kara shiga babbar kasuwar kasar don gudanar da kasuwanci da samun babbar riba.
A bangaren masana’antun kasa da kasa kuwa, wani abu mai muhimmancin gaske shi ne kyakkyawan fata a lokacin da kasuwar duniya ke fama da rashin tabbas. Yayin da wasu makiya ke yada bayanai marasa tushe game da tattalin arzikin kasar Sin, bankin duniya ya yi hasashen cewa, a bana tattalin arzikin Sin zai bunkasa da kaso 5.6%, yayin da OECD kuma ya yi hasashen bunkasar za ta kai kaso 5.4%, kana Asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya yi hasashen bunkasar zuwa kaso 5.2%.
Masu fashin baki na cewa, kwanciyar hankali da dorewar manufofin tattalin arzikin kasar Sin, sun karfafa gwiwar kamfanonin kasa da kasa wajen kara neman shiga babbar kasuwar kasar. Sun kuma yi imanin cewa, kasar Sin na daya daga cikin manyan kasashe a duniya da ke samar da damammakin ci gaba ga kamfanonin kasa da kasa. (Ibrahim Yaya)