Takardar bayanin da cibiyar ilmin fasahar muhimman bayanai da fasahar sadarwa ta kasar Sin (CAICT) ta fitar Alhamis din nan, ta nuna cewa, darajar masana’antar manyan bayanai ta kasar Sin ta samu ci gaba matuka.
Takardar bayanin ta yi nuni da cewa, a shekarar 2021, adadin rahotannin da aka wallafa a fannin manyan bayanai a kasar Sin, ya kai kashi 31 cikin 100 kan na duniya, kuma jimillar mallakar fasaha da aka amince da su da suka shafi manyan bayanai, sun kai sama da kashi 50 cikin 100 kan na duniya. Abin da ya sanya ta zama ta farko a duniya.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)