Gwamnatin Jihar Kogi a ranar Asabar, ta ce, babu wani barkewar wata cuta a kowani sansanin ‘yan gudun hijira da suke jihar a sakamakon ambaliyar ruwa da jihar ta fuskanta.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Zakari Usman shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke zagayen duba barnar da ambaliyar ruwa ta yi a sansanin ‘yan gudun hijira a jihar.
Ya ce, dukka da halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta dauki kwararan matakan da suka dace wajen kare lafiya, inda ya ce babu barkewar wata cuta.
Ya ce, sun dauki jami’ai na musamman da suke duba lafiyar al’umma musamman sansanin ‘yan gudun hijira domin karesu daga cutuka masu yaduwa.
Kwamishinan wadda ya yi zagayen tare da tawagar lafiya na ma’aikatarsa, ya jajanta wa wadanda ambaliyar ruwa ya shafa.
Ya ce, gwamnati ta damu sosai da halin da ‘yan gudun hijira ke ciki, wannan dalilin ne ma ya sanya suke kula da su yadda ya kamata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp