Robar hanci (Nasogastric tube), wani siririn tiyo ne na roba; wanda ake zira shi ta kofar hanci har zuwa cikin tunbi. Manufar ita ce, don a samu kai wa ga cikin tunbi.
Sanya robar hanci, na iya zama cikin muhimman ayyukan taimakon gaggawa; yayin da aka garzaya da mara lafiya zuwa asibiti.
- Kauyuka Suna Kokarin Neman Cimma Burin Samun Wadata Tare A Kasar Sin
- Bukatar Sanin Hakikanin Halin Da Tattalin Arzikin Nijeriya Ke Ciki
Haka nan, sanya robar hanci na da muhimmancin gaske ga mara lafiya kamar haka:
1- Ana amfani da robar hanci, domin ciyar da abinci ko shayar da abin sha ga mara lafiya, musamman a halin da mara lafiya ya tsinci kansa na rashin iya cin abinci ta bakinsa; ko dai saboda mara lafiyar ya ki ci ko ya ki sha ko saboda miki ko rauni a bakinsa ko kuma bayan tiyata a baki ko kuma a makogwaro.
2- Ana amfani da robar hanci, domin bai wa mara lafiya magunguna kai tsaye zuwa cikin tunbinsa, musamman ga mara lafiyar da ke fuskantar wahalar hadiya ko kuma ba zai iya karbar magani ta baki ba.
3- Ana amfani da robar hanci ga mara lafiyan da ya fita daga hayyacinsa, ko dai saboda wata larura ko kuma allurar kashe-ciwo da ake yi kafin tiyata.
4- Haka nan, ana amfani da robar hanci domin kiyaye wa mara lafiya shakar abinci, abin sha, majina ko kuma yawu zuwa cikin huhunsa, musamman ga mara lafiyan da ya gaza hadiyar abin ci ko sha yadda ya kamata; kamar masu shanyewar barin jiki, buguwar kai da sauran makamantansu.
Domin shakar abinci ko abin sha, majina ko yawu zuwa cikin huhu; na da hadarin gaske. Sau da yawa, ba larurar da ta kwantar da mara lafiya ce ke sababin mutuwarsa ba; face illolin shakar wadannan abubuwa zuwa cikin huhu. Hakan na nufin wahalar shakar oksijin.
5- Har wa yau, ana amfani da robar hanci wajen zuke gurbataccen abinci ko abin sha, iska, diwa ko jini daga cikin tunbi.
6- Bugu da kari, robar hanci na amfani wajen bude hanya; bayan toshewar hanyar makoshi daga baki zuwa cikin tunbi.
7- Bayan nan, ana amfani da robar hanci kafin ko bayan tiyata a ciki da dai sauran wasu dalilai daban-daban.
Sai dai, sanya robar hanci ga mara lafiya na daga cikin abubuwan da ke sanya tsoro da fargaba a zukatan ‘yan’uwa da abokan marasa lafiya, saboda yadda ake zaton cewa; ba a sanya robar hanci ga mara lafiya, har sai ya kai gargara.
Sau da dama ma, wasu na canfa cewa; matukar aka sanya wa mara lafiya robar hanci, to fa ba zai dawowa gida ba; ma’ana mutuwa zai yi.
Amma kwata-kwata, abin ba haka yake ba. Domin kuwa, ana sanya wa marasa lafiya robar hancin ne kadai; idan bukatar hakan ta zama dole, sannan kuma sanya ta ga mara lafiyar wani gagarumin taimako ne domin ceto ransa.
Har ila yau, ana sanya robar ne na dan wani lokaci gwargwadon bukata, sannan a cire bayan bukatar ta gushe.
Bugu da kari, babu wani dalilin tsoro ko fargaba; idan aka sanya wa mara lafiya robar hanci, domin yin hakan shi ne abin da zai fi amfanar da lafiyarsa a daidai wannan lokaci.
Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya, marasa lafiyar kuma na gida da na asibiti, Allah ya ba su lafiya; ya kuma tashi kafadunsu.