Babban jami’in gudanarwa na kamfanin kula da albarkatun mai na kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya jaddada cewa, babu maganar dawo biyan tallafin mai gaba daya a Nijeriya.
Ya shaida hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja bayan wata ganawa da ya yi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
- Rikicin Falasdinu Da Isra’ila: Saudiyya Ta Dakatar Da Duk Wata Tattaunawa Da Isra’ila
- Ba A Dakatar Da Mele Kyari Ba —NNPCL
Idan za a tuna dai, shugaban kungiyar (PENGASSAN), Festus Osifo, a ranar Jama’a ya yi ikirarin cewa, gwamnati ta dawo da biyan tallafin mai, duk da cewa, gwamnatin ta janye tallafin man ferur din tun a watan Mayu.
A nasa jawabin, Shugaban kamfanin NNPCL Kyari, ya yi bayanin cewa, sayar da mai da ake yi a wasu jihohi akan farashi mai sauki ba shi ke nufin an dawo da biyan tallafin man fetur ba.
Dangen da dogon layukan mai da ake samu a wasu gidajen mai a sassan kasar nan, Kyari ya ce, matsalar ta samu asali ne sakamakon rufewar wasu hanyoyin da man ke bi zuwa matattararsa na arewacin kasar da ya ke taso wa daga kudancin kasar nan, hakan ya janyo tsaikon samar da isashshen man a wasu wurare.
Ya kara da cewa, tsere a tsakanin ‘yan kasuwa masu sayar da man a gidajen man ne ya janyo raguwar farashin mai a wasu gidajen man.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp