Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Nasarawa, Dakta Aliyu Bello, ya ce jam’iyyar tana da haɗin kai kuma tana ci gaba da samun nasara a ƙarƙashin Gwamna Abdullahi Sule.
Ya bayyana haka ne a sakatariyar jam’iyyar da ke Lafia, lokacin da ya tarbi Sanata Aliyu Wadada, wanda ya koma jam’iyyar daga SDP.
- An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba
- NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi
Dakta Bello ya ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa cewa APC ta rabu gida biyu.
Ya ce, “Jam’iyyar APC tana zaune lafiya, kuma tana ci gaba da samun nasara. Waɗanda ke yaɗa maganar rabuwar jam’iyyar masu niyyar tsayawa takara ne.”
Ya ƙara da cewa, duk wanda yake son zama ɗan jam’iyyar ko kuma wanda ya dawo, dole ne ya yi rijista a sakatariyar jam’iyyar ta jiha.
“Sanata Wadada yana cikin rijistarmu tun da farko, kawai mun sake ba shi sabon katin zama mamba ne. Don haka, barka da dawowa gida,” in ji shi.
Dakta Bello ya ce APC za ta ci gaba da karɓar duk wanda ke son dawo wa jam’iyyar kuma yana kishin ƙasar nan.
A nasa ɓangaren, Sanata Aliyu Wadada ya ce dawowarsa jam’iyyar APC kamar komawa gida ne, domin yana daga cikin wanda suka kafa APC a Nasarawa.
“Ina cikin jam’iyyar SDP, amma ban daina goyon bayan ci gaban APC ba. Ba mu bar jam’iyyar gaba ɗaya ba, kawai mun ɗan huta na wani lokaci ne. Yanzu mun dawo,” in ji shi.