A wannan makon mun kawo muku ci gaba da hirar da muka yi da daya daga cikin fitattun Jaruman fina-finan Hausa cikin masana’antar Kannywood, kuma Jarumi mai taka rawa a cikin shirin Dadin Kowa na Arewa24, wanda ya shafe shekaru sha biyar a cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, MUHAMMADU MURTALA wanda aka fi sani da DANTANI MAI SHAYI. Ya warware zare da abawa game da abubuwan da masana’antar ke bukata, ga dai yadda hirar ta kasance kamar yadda Wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA ta kawo mana.
Ya akai ka tsinci kanka a cikin shirin Dadin Kowa?
Yadda aka yi na tsinci kaina a cikin shirin Dadin Kowa bana mantawa da watarana ina zaune Nazeer Adam Salihi ya kira ni ya ce; Akwai wani gidan Tibi da za su fara wani shiri (Da yake su marubuta ne kuma yana daya daga cikin daraktocinmu na lokacin dana fara harkar wasan hausa, irin kungiya haka sitejin dirama, lokacin yana rubutu), Sai ya yi mun tayi ya ke cewa ya sanni domin darakta na ne tun muna koyo, zan iya ruke rol din mai shayi. Na ce “kowanne rol ka bani zan iya rukewa”, wannan shi ne asalin dalilin fara mai shayi na. Na je nayi intabiyu, shi daraktan T. Balarabe Bozi ya ce na dace nayi daidai, tun daga nan kuma na kasance mai shayi har iyanzu, amma a Dadin Kowa.
Amma mene gaskiyar maganar da wasu suke rade-radin cewa har a zahiri dama can kana shayin?
Gaskiya kin bani ‘yar dariya, a zahirin gaskiya ba shayi nake siyarwa ba, wannan sana’a ce ta fim shi ne nake shayi a Dadin Kowa, amma ni in ka ce ma in yi shayi ban san yadda ake yin shi ba. Sana’a ce dai kawai ta fim, babu irin rol din da bana bugawa. A wani fim da muka yi na Sarkin Barayi ni da Bosho ne dan sanda, mu kama Sadik Sadik, mu kama wannan mu kama wancen, karshe ashe kajin da nake ci na gidana aka kamo aka soya muke ci ba mu sani ba, to duk irin makamancin wannan mukan yi. Kin ga kamar a Aliya da nake fada miki na Ali Jita kwanan nan ya fara fitowa a maigadi na fito, amma fa maigadin fitinannan mai gadi ne har ‘yan gidan ban bari ba, toh duk dai makamancin wannan.
Wanne irin rawa ka fi son takawa, kuma me ya sa?
Ni yanzu a fim ba irin rol din da za a bani da ba zan yi shi ba, zan fito a gurgu, zan fito a komai ma, saboda ni na yi sitejin dirama. Ita sitej dirama abu ne wanda za ka yi shi a gaban Jama’a ba kunya, ka fito ka yi dirama kuma jama’a sun taru sai ka ba su dariya, to na yi wannan, ni ba rol din da za a bani na kasa taka shi sai dai in rol din ba na arziki ba ne. Sai dai na fi son Komedi me abun bada dariya gaskiya.
Ko akwai wani fim da ya taba baka wuya?
Wani fim ne kwanan nan muka yi shi Dan Majalisa ya ban wahala fim din, domin an ce mun na gama ya kai sau nawa, a ce mun na gama kuma ina shan wahala a fim din, in na fita tun safe in aka doran kyamara har dare har sai da ya fita daga raina, har sai da na zo ina fada da me fim din ma, ya ban wahala gaskiya fim din. Saboda sai a ce mun na gama sai a kira ni a ce dan Allah saura sin uku, to sai in yi sin goma sha biyar, wannan abin ya ban wahala sai da na rame wallahi, na zo muka je muka kwan daya, wallahi ban bacci ba ga sauro ga waye duk, gaskiya ba zan taba mantawa da wannan fim din ba, shi ya ban wahala.
Wanne fim ne ka fi so wanda ya zamo bakandamiyarka?
Bakandamiyata shi ne Dadin Kowa, ina ji da Dadin Kowa, ina son shi da shi da Sarkin Barayi ina sonsu, domin na fi buga rol sosai.
Wanne waje ka fi so a cikin shirin Dadin Kowa?
Wajen da muke fada da Sallau, na fi jin dadin wannan
Wanne irin kalubale ka taba fuskanta cikin masana’antar?
Eh! To kalubale ba wanda ba za ka fuskanta ba, za ka fuskanci kalubale da dama, domin wasu idan ba dan kaffaninsu bane kai kiri-kiri za ka ga ba za a saka a fim dinsu ba, sai kuma kalubale na biyu amma shi ga jama’a ne, a kulli yaumin kana harkar fim kallon mai kudi suke yi ma, wannan shi ne babban kalubale, ba za ka taba cewa ba kada kudi a yarda ba, sai a ce haba ku da ku ke fim musamman ma da ku ke Arewa24 ai a cikin kudi ku ke da sauransu. Ba za ka taba cewa mutum ba kada kudi ya yarda ba, sabida shi kawai yana ganinka a Tibi shi kullum kallon kudi ya ke yi maka, wannan shi ne babban kalubale
Za mu ci a mako mai zuwa