Duk da kace nace da al’umma keyi dangane da masana’antar Kannywood akan bata tarbiyyar matasa da sauran al’umma da suka ce masana’antar Kannywood ta ke yi,jarumi kuma mai shirya fina finai a masana’antar Kannywood Tijjani Asase a wani faifan bidiyo da ya fitar ya bayyana cewar babu wata masana’antar shirya fina finai a Duniya da take da tsafta kamar Kannywood.
Yayin daukar faifan bidiyon an hango Tijjani wanda yana daya daga cikin shirin fim mai dogon Zango mai suna A Duniya yana cewa ya gode Allah madaukakain Sarki da ya nufeshi da zama dan Jahar Kano kuma dan masana’antar Kannywood domin kuwa a duk fadin Duniya hatta da birnin Madina na kasar Saudi Arabiya babu inda ake harkar fim mai tsafta kamar yadda akeyi a wannan masana’antar ta Kannywood dake da helkwata a birnin Kano.
- Ƙarancin Wayewa da Samar Da Labaru Masu Kyau Ke Durƙusar Da Kannywood
- Lamunin Naira Biliyan 5 Ga ‘Yan Fim: Yaushe Kannywood Za Ta Samu Nata?
A kwanakin baya dai gwamnatin jahar Kano ta dakatar da cigaba da nuna shirin fim mai dogon zango na A Duniya wanda Tijjani Asase na daga cikin manyan jarumai a cikin wannan shiri,inda ta bayyana cewar ta dauki wannan mataki ne sakamakon abinda ta kira kwabar da ake tabkawa a cikin shirin da ka iya bata tarbiyyar matasa da zata kaisu ga shaye shaye da sauran miyagun halaye.