Wani jigo a jam’iyyar APC kuma shugaban ƙungiyar masu ruwa da tsaki ta ƙasa, Barista Ibrahim Abdullahi Jalo, ya bayyana cewa labarin da ake yaɗawa cewa Kashim Shettima ya yi murabus ko yana da matsala da Shugaba Tinubu ba gaskiya ba ne.
Ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya kira a Abuja, inda ya ce wasu mutane ne kawai ke ƙoƙarin tada zaune tsaye da yaɗa labaran ƙarya domin haifar da matsala.
- Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur
- Mata Sun Yi Zanga-zanga Kan Yawaitar Satar Mutane A Kogi
“Ba gaskiya ba ne cewa Shettima ya ajiye aiki ko yana da saɓanin da Shugaba Tinubu.
“Shettima mutum ne mai natsuwa kuma ba ya rigima da kowa. Ayyukansa kawai yake yi ba tare da hayaniya ba,” in ji Jalo.
Barista Jalo, ya ce da wannan labari gaskiya ba ne, inda ya ce babu wani saɓani a tsakaninsu.
Ya ce a siyasa akwai nau’ukan mutane uku – masu gaskiya, maƙaryata, da masu son tada zaune tsaye.
Ya ce su a matsayinsu na ‘ya’yan jam’iyyar APC na gaskiya, suna goyon bayan Tinubu da Shettima, kuma idan akwai kura-kurai, suna ganin ya kamata a gyara ne, ba a lalata komai ba.
Dangane da raɗe-raɗin cewa ana shirin sauya Shettima kafin zaɓen 2027, Jalo ya ce wannan ma labarin ƙanzon kurege ne.
Ya ce jam’iyya tana da hanyarta na sauya mutum, amma babu wani abu makamancin haka yanzu.
Ya ƙara da cewa suna jiran 2031 domin Shettima ya fito takarar shugaban ƙasa.
Har ila yau, ya buƙaci masu yaɗa jita-jita da su janye maganganunsu, su jira domin idan akwai matsala, za ta bayyana kanta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp