Shugaban Rundunar Sojin Sama (CAS), Air Marshal Hasan Bala Abubakar, ya umurci kwamandojin rundunar sojin sama da su ci gaba da mamaye yankin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya, Kudu maso Gabas, da Kudu maso Kudu, inda ya bayyana cewa, ‘yan ta’adda ba za su samu mafaka ba, a dare ko rana.
A wata sanarwa da kakakin rundunar NAF, Air Cdre Ehimen Ejodame, ya fitar, ya ce, kara kaimin rundunar saman ya biyo bayan sauya dabaru da kuma tsauraran matakan hadin gwiwa tsakanin sassan sama da na kasa, musamman a rundunar ‘Operation HADIN KAI (OPHK)’ da sauran ayyukan rundunar hadin gwiwa a fadin kasar.
- Adamawa Ta Amince Da Mafi Ƙarancin Albashi Na ₦70,000 Ga Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi
- Gwamnatin Kano Ta Yi Barazanar Hukunta Matasa Masu Janyo Rikice-Rikice
Ya ce, rundunar sojojin saman Nijeriya (NAF) ta kara kaimi wajen gudanar da sintiri ba dare ba rana, tare da kai munanan hare-hare ga ‘yan ta’adda da masu tayar da kayar baya.
Air Marshal Abubakar ya ba da misalin harin da sojin saman suka kai, inda suka dakile harin ‘yan ta’adda a sansanin soji na ‘New Marte’ da sanyin safiyar ranar 24 ga Mayu, 2025, a jihar Borno
A wannan rana, gungun mayakan ISWAP sun yi yunkurin kutsawa sansanin soji ta hanyar amfani da babura da jefa bama-bamai (VBIED).
Jiragen NAF ne ke bayar da bayanan sirri kan duk wata zirga-zirgar masu tada kayar baya a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp