Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin, Zhang Xiaogang ya fitar da sanarwa kan batutuwan da suka shafi aikin soja a baya-bayan nan. Ya ce, Taiwan wani bangare ne na kasar Sin. Kuma babu wata tsokana da sojojin Amurka za su yi da za ta iya canza wannan lamari, sabanin haka, za ta iya nuna munafuncin da Amurka ta dade ta na yi ga al’ummomin duniya, kuma za ta iya kara karfafa niyyar jama’ar kasar Sin ta kare ikon kasa da cimma cikakkiyar dunkulewar yankunan kasar baki daya.
Game da zarge-zarge marasa tushe da sabon ministan tsaron Amurka ya yi kan Sin, Zhang Xiaogang ya ce, Sin na adawa sosai da hakan. Kuma jama’ar kasar Sin na son zaman lafiya. Bugu da kari, ya ce a ko da yaushe, bangaren Sin ba zai tayar da yaki don habaka kasar ba, kuma ba zai yi watsi da iko da moriyarsa ba, kana zai tsaya tsayin daka kan tinkarar duk wata barazana da kalubale.(Safiyah Ma)