Alkalin babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, Ahmed Mohammed ya sanya ranar 30 ga watan Agustan 2023 domin yanke hukunci kan karar da tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya shigar a gabanta bisa bukatar da a dakar da bincikensa.
A cikin takarardar karar mai lamba: FHC/ABJ/CS/753/2023, ta na tuhumar hukumar tsaro ta cikin gida DSS, rundunar ‘yansanda, hukumomin ICPC da EFCC, NIS da kuma Atoni Janar na kasa a matsayin masu karar Gwamna Matawalle.
Matawalle, wanda ya kasance daya daga cikin wadanda shugaban kasa Bola Tinubu ya mika wa Majalisar Dattawa sunansa don a nada shi a mukamin minista, ya nemi kotun da ta dakatar da masu kararsa ne bisa duba ga hukuncin da mai shari’a Alkali Aminu Aliyu ya yanke a ranar 31 ga watan Mayun 2023 a kara mai lamba: FHC/GS/CS/30/2021.
Hukunci ya dakatar da duk wata hukuma kan bincike kai tsaye ga tsohon gwamnan ko iyalinsa ko mataimakansa a gudanar da gwamnatinsa dangane da yadda aka kashe kudaden gwamnatin jihar.
Kazalika, duba da sashi na 4, 6, da na 7 na dokar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Zamfara mai dauke da lamba 12 ta shekarar 2021, Matawalle ya nemi kotun da ta yanke hukunci na cewa, babu wata hukuma da ke da ikon bincikensa akan maganar zargin cin hanci da rashawa.