Tsohon gwamnan jihar Sakkwato Attahiru Bafarawa ya bayyana sanarwar fita daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP domin assasa sabuwar tafiyar matasa.
Bafarawa ya bayyana ficewa daga jam’iyyar ne a cikin wata wasika da ya rubutawa shugaban jam’iyyar PDP na kasa wadda ta bulla a ranar Talata.
- JAMB Ta Musanta Zargin Kashe Naira Biliyan 9 Wajen Ciyarwa Da Walwala
- Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar Da Ɓullar Cutar Murar Tsuntsaye A Kano
Babban jigon dan siyasar wanda ya mulki jihar Sakkwato a matsayin gwamna a wa’adin mulki biyu a jam’iyyar ANPP daga 1999 zuwa 2007 ya bayyana cewar a tsayin shekaru ya bayar da gudunmuwar bunkasa PDP wadda ya shiga a 2014.
Ya ce duk da cewar fita daga jam’iyyar mataki ne na kashin kansa amma ba mai sauki ba ne wanda ya dauka domin mayar da hankali kan sabuwar tafiyar bunkasa al’umma musamman matasa.
Tsohon dan takarar na shugabancin kasa a jam’iyyar DPP ya fita daga PDP ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke fama da matsanancin rikicin cikin gida wanda ke neman kassara jam’iyyar a yayin da wasu jigogin siyasar kasar ke kawancen karbe mulki daga APC a 2027.