Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a majalisar ɗinkin duniya, ya bayyana a ran 13 ga wata cewa, kasashen da suka ci gaba suna ɗauke da ɗawaiya ta asali kan sauyin yanayi a duniya, kuma ya kamata su jagoranci rage hayakin da ake fitarwa sosai, tare da cike giɓin dalar Amurka biliyan 100 a duk shekara, a matsayin kuɗin ba da gudummawar ga sauyin yanayi. Haka kuma, bai dace su aiwatar da manufar ba da kariya ga cinikayya bisa fakewa da kare muhalli ba.
Zhang Jun ya ce, wasu kasashen da suka ci gaba sun saɓa wa ƙa’idojin hukumar cinikayya ta duniya WTO, da kawo cikas ga tsarin samar da kayayyaki da jigilar kayayyaki, da gurgunta ƙoƙarin da kasashen ke yi na cimma burin ci gaba mai dorewa, da cin karo da ƙoƙarin haɗin gwiwar kasashen duniya na magance sauyin yanayi.
Ya ce, manufar ba da kariya ga cinikayya bisa fakewa da kare muhalli, ta zama wata sarƙar da ta ɗaure kasashe masu tasowa, yayin da haramtaccen takumkumi ya kasance sauran sarƙar da ke dagula ci gaba da zaman lafiyar kasashe masu tasowa. (Mai fassarawa: Yahaya)