Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, ya kamata a bi kuduri mai lamba 2758 na babban taron MDD, a kaucewa saba ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya”.
Wang Wenbin ya bayyana cewa, a ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 1971, aka zartas da kuduri mai lamba 2758 yayin babban taron MDD karo na 26, kudurin da ya tabbatar da mayar da dukkan hakkin jamhuriyyar jama’ar kasar Sin, da amincewa da gwamnatinta a matsayin halaltacciyar wakiliyar kasar Sin daya tak a MDD, kana aka bukaci wakilan hukumar yankin Taiwan da su janye daga MDD.
Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, a shekarun baya-baya nan, wasu mutanen Amurka sun nuna ra’ayoyi da suka sabawa kuduri mai lamba 2758, da yada jita-jitar wai kudurin bai daidaita matsayin yankin Taiwan ba, da yin biris da ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya”, da goyon bayan ayyukan ‘yan aware a yankin Taiwan, wanda zai kawo babbar illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin.
A cewarsa, babu shakka kasa da kasa ba za su amince da irin wannan aiki ba, kana yunkurinsu zai ci tura domin Sinawa suna da imani da tabbataci kan ikon mulkin kasar da cikakkun yankunanta. (Zainab)