Lauyan nan na Kano, Abba Hikima Fagge, ya bukaci Gwamnatin Kano da ta duba Allah ta tsayar da aikin gadojin da ta kuduri aniyar yi a Kano, ta hanyar ɗibar kudaden kananan hukumomi don gina gadoji a birni alhali kauyuka na cikin matsanancin hali da bukatar aiki.
Abba Hikima ya bayana hakan a shafinsa na Facebook a safiyar ranar Laraba inda mabiyansa ke ci gaba da bayana tsokacinsu kan kalaman nasa.
- DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Kori Gwamna Abba Gida-Gida Ta Tabbatar Da Nasarar Gawuna
- Malamai A Kano Sun Gabatar Da Addu’o’i Kan Allah Ya Tabbatarwa Gawuna Nasararsa A Kotun Ƙoli
Hikima ya ce, “Irin wadannan abubuwan da ake dauko wa ke sawa mutane suke daukar gaba daya ashe ‘yan siyasa irinsu daya, ”
“Yanzu saboda Allah ina adalci anan? Kauyukan Kano suna cikin mugun hali, kwanaki Freedom Radio ta yi ta bankado matsalolin kauyukanmu amma a dauko kudinsu a saka a gada guda daya Me wannan kudin?”
“Lallai akwai wani abu da yake faruwa a kasa.” cewar Abba Hikima.