Dakta Ahmad Tujjani Sani Sa’ad, wanda aka fi sani da Al-Azhari, ya bayyana rashin gamsuwarsa da ra’ayoyin al’umma kan cewa malamai su tsame hannunsu a cikin harkokin siyasa saboda matsalolin da ake samu a fagen siyasar Nijeriya.
Dakta Ahmad Al-Azhari ya bayyana haka ne a lokacin wani taro da ya gudana a Zariya da ke Jihar Kaduna.
Ya nunar da cewa, duk wanda ke cewa bai kamata malami ya shiga harkokin siyasa ba, to bai san wane ne malami ba da kuma irin ayyukan da Allah ya dora musu a kan al’umma.
Dakta Al-Azhari ya nuna matukar damuwarsa na yadda al’umma sun yadda da malamai a duk wani abu da ya shafi duniya, amma sai aka wayi gari ana nuna cewa bai dace a saurari malama ga al’amurrar da suka shafi shugabanci da ya shafi siyasa.
Ya ce ya kamata al’umma su dawo kan hankalinsu tare da sanin cewa akwai bukatar malamai su tsumduma cikin harkokin siyasa.