Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce baje kolin Canton Fair dake gudana a yanzu, ya shaida karsashin kasar Sin na bude kofa, da zarafi ga duniya na cin gajiya daga damammakin kasar Sin, wanda hakan ya tabbatar da kwarin gwiwa, da jajircewar Sin wajen ingiza salon zamanantarwa na kasar.
A ranar Asabar 19 ga watan nan ne aka kammala zangon farko na baje kolin karo na 136 na zahiri, inda ‘yan kasuwa na gida da na waje suka gudanar da hada hada daban daban, kuma nasarorin da aka samu sun kai sabon matsayin koli a tarihi, matakin da ya shaida kyakkyawan mafari na baje kolin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp