A yau shafin namu zai yi duba ne dangane da abin da ya shafi Bambancin kalaman soyayya na baya dana yanzu. Idan muka waiwaya baya kadan ba zamanin iyaye da kakanni ba, za mu yi duba ne a shekarun da suka gabata kadan, ta yaddaake sarrafa kyawawan kalamai ta siga daban-daban wanda a yanzu sam! Ba a yin kwatankwacinsu.
Duba da yadda zamani yake sauyawa a kullum, wanda a baya akan sarrafa kalaman soyayya ta kowacce siga har ta kai ga ta birge wanda akai wa su, ko da kuwa kalaman ba su yi dai-dai da wanda ake fadawa su din ba, ana fada ne kawai dan a birge juna, kuma kwalliya na biyan kudin sabulu.
-  Sojoji Sun Kubutar Da Dalibar Chibok Tare Da Tagwaye ‘Yan Watanni 4
- Darajar Vinicius Junior Ta Sake daukaka
Domin kuwa duk masoyin da ya aika wa abokin soyayyarsa sakon kalaman soyayyar, abokansa na murna da ihu gami da shewar nuna jin dadi da birgewa har shi ma masoyin ya yi kokarin tsara nasa kalaman tare da taimakon abokansa, wani sa’in ma akan tsara su ne cikin rubutu me ado da kwalliya a takarda ko littafi.
Kalaman soyayya na baya sun sha bamban da kalaman da ake furtawa a yanzu, kalamai ne irin wanda a yanzu in aka furta wasu sai dai a ci dariya. Misali kamar su; “Kash! Ash! Wash! Kibiyar sonka ta soke ni, me makon jini ya fito sai wasukalmomi guda hudu suka fito; Tuwon lobe, miyar kiss, I wan’t Alayyahun lambun soyayya. Ya zunzurutun muzirarin zoben zinaren zuciyata, ya mamallakin mulkin zuciyata, na zama madara ka zama suga sai mu taru mu gauraye shayin soyayya.
Mutane suna rayuwa, wasu suna mutuwa, wasu su fidda tsammani, wasu su sa rai, wasu su ce sai anjima, wasu za su iya mancewa da kai ni ko har abada ba zan taba mantawa da kai ba, kana cikin zuciyata. Ba zan daina fesheka da turaren kauna ba, har sai lokacin da kayi atishawar bege da kauna. Sonka ya dada samun mafaka a falon gidan zuciyata, wuka za ta iya yanka nama amma ba za ta iya yanka soyayyarmu ba.
Rayuwa ba tare da kai ba babban hadari ce.Na yi mafarki ana ruwan sama ashe ba ruwan sama bane gwala gwalan ‘lobe’ ne ke zuba, ka zama wata na zama zara mu taru mu haskake duniyar soyayyarmu. Ka sani ya ma’abocin kyau jinina ya daina aiki a lokacin da na gan ka, idanuwana sun makance a dalilin kyawunka, kunnuwana sun kurmance saboda zakin muryarka, komai nawa ya daina aiki har sai na ji wadannan kyawawan kalaman daga bakinka sannan komai nawa zai dawo daidai ya masoyina. So, sobe ka, Kauna, amincewa, yarda, bege, Yabo, a gare ka ya masoyina.
Begen me bege da fatan wanda ake begen yana begen me begensa”.Wannan a takaice kanan, wanda a yanzu kalamai ba su fiye tasiri a zukatan wasu masoyan ba, musamman yadda karya da yaudara ta mamaye zukatan masu yinta, kana suka yawaita, duba da yadda zamanin yake kara sauyawa a kullum, mayaudaran masoya na karuwa fiye da masoyan gaskiya.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin mabiyansa, ko ya bambancin kalaman baya da na yanzu suke? Ko kalaman soyayya na tasiri a cikin soyayya har ta kai ga tasace zuciyar wanda ake so a yanzu?, Ko kana/kina daga cikin wadanda kalaman soyayya ke saurin sace musu zuciya?, Wadanne kalmomi ne ka fi so, ko kika fi so wanda suke saurin saka ki/ka nishadi? Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Hamidan Badamasi daga Jihar Kano Rijiyar Lemo, 07061855550:
Babu shakka akwai bambanci metarin yawa cikin kalaman soyayyana da da kuma na yanzu mafi yawan kalaman da ake amfani dasu a bayakalamai ne masu nuna kunya da dattaku, kuma kalamai ne da ko a ina kana iya furtawa wanda kake kauna, su ba kamar kalaman yanzu da mafiya wancinsu rashin kunya da fitsara suka yi yawa ba, Kalaman soyayya nada; Sahiba ta, Abar kaunata.
Kalaman soyayya na yanzu; Lambar yabo gareki me sona, Tauraruwa hasken ruhina, Gimbiya Alkairin rayuwata. Ai saia n gina soyayya akan gaskiya sannan kalamanta ke yin tasiri duba da yanayin yadda samarin da ‘yan matansuka zama ‘majority’ soyayyar ba gaskiya ta kunsa ba dan haka ni banaganin har yanzu kalaman suna tasiri,babu shakka ina cikin wanda kalaman soyayya ke saurin sace musu zuciya, amma hakan yanada alaka ga wandda kalmar ta fito daga bakinta, Na yi kewar rashin ganinka kwana biyu, na daga cikin kalaman dake saurin sanyani farin cikin a duk lokacin dana tunasu.
Aisha Sani Abdullahi Zayishatulhumairath Jihar Jos Marubuciyar Hausa:
Tabbas akwai bambanci domin a da kawai ana tsara kalamai barkate ba tare da nazarin kasancewar su na hakika daga zuci ba, yanzu kuwa ana amfani da abun da ke zuciya ne kawai, domin bayyanar da tsantsan soyayya.
A da ana yawan amfani da su kamar haka; “ke ce abincin raina, fitil a rayuwa” da sauran su, yanzu kuwaan samu ci gaban tsarawa kamar; “Ba yau ko dukiya zan so ba zan soka ne saboda ka dauke ni tamkar sarauniya, hakan na bani tabbacin cewa babuwata da za ta iya kasancewa a cikin zuciyarka, bayan ni, ina sonka ina kaunar, a duk inda kake ka tuna cewakai ne farin cikina”.
Tabbas! kalaman soyayya na da matukar tasiri domin yana faranta ran masoya tare da tunartar da su asalin son da ake yi masu, Mussamman ya yin da aka tura sakon bazata.
Tabbas! ina ciki domin ina jin dadi da farin ciki yayin da muradin raina ya turominsakon kalaman Soyayya.
Kalaman masoyina duka suna mun dadi kuma kullum cikin tuna su nake a raina sunayawo cikin kwakwalwata don kuwa zantukansa kai tsaye daga zuciya yake furta mun.
Abdul’azeez Yareema Shaheed (Dan Amar) daga Jihar Kano:
Akwai bambanci sosai tsakanin kalaman soyayya na yanzu da na baya, domin na da an fi fadar kalaman gaskiya kuma ya fi sa nishadi, na yanzu kuwa babu wani fikira a ciki sai tarin yaudaran kalamai.
“Ke ce Turmi sha dakan gidana”, Kalaman soyayyar da kenan. Na yanzu kuma; “Ni daga kena kulle shafin soyayya da ‘yan mataban dama na zamo angon ki ni ba zan miki karya ba”.
Kalaman soyayyar yanzu ya fi tsayi da dadin fada a baki. Kwarai kuwa kalaman soyayyaya na da matukar tasiri a cikin soyayya har takan sace zuciyar mutum farat daya.
Kwarai kuwa ina cikin mazan da kalaman soyayya ke sace zuciyarmu. Kalaman da nake so wanda nake tunaninsu shi ne; so da so kaunaya fi so akwai ciwo zafi, zama da kai Yareema ya sa ni nishadi, kai gwarzo ne cikin samari.
Nura Rabi’u daga Jihar ZamfaraTalatan Mafara:
Akwai bambancin kalaman soyayya na da dana yanzu, kalaman daake yi yanzu da ba a yinsu.
A lokutan baya ana amfani da; “Ina sonki kinasona za a amince a lokutan yanzu kalaman sun yi yawa har da na karya.
Eh! kwarai suna yin tasiri a zuciyar masoya fiye da tunanin mai tunani. Eh! ina ciki saboda idan masoyinka bai fada maka kalmar so mai dadi ba zai wahala ka amince da shi.
Duk macen da ta ce tana sona tsakaninta da Allah idan ta ce za ta zauna da ni duk rintsi duk wuya wannan yana tasiri a zuciyata.
Maryam Ismail Ibrahim (Jorderh majidadi) daga Jihar Katsina:
Akwai bambanci sosai a tsakanida sauye-sauye na zamani. A da mafi akasari duk kalaman da za ka gani da yaren Hausa ne sabanin yanzu da turanci ya kwace, komai yawancin kalaman yanzu na kasancewa da turanci.“Kin kasance farin cikin rayuwata, wani bari kuma abun alfahari a gare ni bana tunanin zaniya kasancewa a duniyar nan idan har babu ke a gefe na.‘You’re the lobe of my life. Also my happiness. You’re the only one in my heart no one more now and foreber”.Kwarai da gaske Kalaman soyayya na taka muhimmiyar rawa a bangaren soyayya, ta kan sace zuciyar wanda ake wa ko ince takan aika sakon da satittuka a cikin dakiku kadan.Gaskiya bana cikin wanda kalaman soyayya ke saurin sace zuciyata, duk da ba zance ba sa burge ni ba, amma ba sa satar zuciyat a ko kadan. In dana jisu a nan nake barinsu. Kalaman da nafi so duk bana jerin soyayya a ciki, babu abin da ya kai ac e Allah yayi maka albarka dadi, wannan kalamain a albarka suna matukar narkar da zuciyata.Hafast Yusuf Muhammad:
Akwai bambancin soyayyar da da ta yanzu da ba su kai kalamai kamar na yanzu ba, saurayin yanzu ko ba aurenki zai yi ba zai miki kalamai masu dadi da za su saka ki jin dadi, zaki so shi, na da kuwa ba su san kalamaiirin na yanzu ba, amma soyayyyar da tafi karko ta yanzu kuwa wata ma da ita gunda babu sai dai Allah ya sa mu dace Ameen.
Lokacin baya ana amfani da kalamai misali “Ya zunzurutunmazirarin zuciyata, Ya abin kaunata,in ba kai ba sai rijiya”.
Lokutan yanzu kuma; “My sweetheart, my hubby,my dear my soul”. Gaskiya kalamai suna ratsa zuciyar masoya kana jin dadi kana annashuwa a lokacin sai da Allah ya ganar da mu.
Kalmar da take ratsamin zuciya ita ce “my sweetheart,my honey”.
Hadiza D. Auta daga JiharZamfara:
Akwai bambanci a tsakaninkalaman soyayya na yanzu da nabaya. Domin a baya wato su kawai ake yi tamkar zubar ruwa ba a yaballe wakafi. Sabanin na yanzu dasuke tafiya cikin sanyi da kwantar dazuciya.
A can baya ana fadin “Ya kaiazurarin azurfar makwallaton zuciya, mai luguden dakan uku-uku a cikinfarfajiyar dandamalin fadar zuciya”.
A yanzu kuma ana furzo kalamai masu tafiyar da zuciya kamar haka; “Ahankali ina ta ba ka filayen zuciyatai na kuma so in rasa kaina a garin yinhakan ta yadda ba zan taba samuwaba, sannu-sannu ina ta mika rayuwatazuwa gare ka masoyina, saboda kazama abin kaunata wanda nake tunakaramcinka a gare ni yayin da na kekara kusantuwa da kai cikin tunane-tunane na,wadanda suke fara bayyana zamanka masoyina abin kaunata, kai giza-gizai ne a inuwata kuma kairuwan sama ne masu jike ni da farinciki mayalwaci, ina kallonka kamar iska wanda ke tafiya da tunani kuma ya sabunta mini kaddarata ta hanyar samar da sabuwar safiya a rayuwata.
Sosai kalaman soyayya suna da tasiriwajen sace zuciyar ma’abocin son, musamman idan mai yinsu ta san hanyoyin sace zuciya cikin sauki.
Tabbas! ina cikin, domin ita maganamai dadi ko a cikin Addininmu na Musulunci sadaka ce, in ji Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.
Akwai da yawa wadanda ke saurin tafiyar da zuciyar kowa ma matukar an san ta kan furta su cikin ruwan sanyi tare da kwantar da murya.
Abba Abubakar Yakubu, Shugaban Kungiyar Jos Writers Club:
Soyayyar Yanzu ta sha bamban da ta Da, babu shakka yadda matasa a shekarun baya suka gudanar da al’amarin soyayyar su tsakanin saurayi da budurwa abu ne mai matukar ban sha’awa, duk da yake ba za a ce ta da ta fi ta yanzu armashi ba, saboda lokaci ne daban-daban, kuma kowanne lokaci da irin na sa tsarin zamantakewar.
A shekarun baya ga wadanda suka shaida wannan lokacin ko aka ba su labari, ana musanyen kalamai ne na soyayya a wasika, har ma wadanda ba su yi boko ba, kan je wajen wasu abokansu don su rubuta musu kalmomi masu rikita zuciyar masoyiya, ko da kuwa azahiri wasu kalaman ba su yi kama da gaskiya ba, amma jin su yana kwantar da hankalin wandaaka aikawa, da sa nishadi a zuciyar mai karatu. Na tuna a lokacin har ma wasu na hayar abokimai baki da ya iya kalaman soyayya don ya yimusu rakiya wajen budurwa, domin ya tayasu tsara ta da kalaman soyayya masu saurin shawo kan zuciyar budurwa.
Mata da yawa zakin baki da kalaman soyayya masu dadi sune suka yaudare su ga son wanda daga bisaniya yi nasarar aurensu, ko da kuwa ba shi ne yafi dacewa da su ba.
A wadancan shekaru ina iya tuna wani marubuci, Aminu Abdu Na’Inna da ya yi wasu littattafan soyayya, ciki har da wani bakandamiyar sa SO MARURUN ZUCIYA, wanda ke kunshe da wasiku masu kunshe da kalaman soyayya masu daukar hankali da ke kwatanta masoyiya da tauraruwar da ke haskaka birnin zuciya, wacce kallonta ke dauke numfashin duk wani mai kallonta, wacce kamshinta ya fi turare dan goma, wacce komai duhu in ta fito ko ina haske yake yi kamar wata daren goma sha biyu.
A shekarun baya samari da ‘Yan mata sun ci kasuwar irin wadannan zafafan kalamai, kuma gwanayen sarrafa harshe da azancin maganaa wancan lokacin sun burge soyayya sosai.
Amma a yanzu yanayi ya canza, samari da ýan mata sun daina kallon irin wadannan kalamaina kururutawa a matsayin wani abin burgewa. Zaurukan sada zumunta, sun maye gurbin wasiku.
A yanzu an fi amfani da gajerun kalmomina kai tsaye, da ke nuna kulawa da nuna damuwa da mutum.
‘Yan mata sun gane saurayi ya kira sua waya da safe da rana da yamma, kuma a raba dare ana hira ta WhatsApp, don a ji yaya suka tashi, yana suka wuni, ko sun ci abinci, ko sun je makaranta, ko za a fita da su shaÆ™atawa, ko mai suke bukata na kwalama da sauransu.
Abubuwan burgewa da daukar hankali sun fi rinjayar ‘yan mata, a maimakon dogayen kalmomin soyayya.
Mawakan zamani sun dauke wahalar da samari a baya suka sha ta tsara kalamai kafin su je hira wajen budurwa, yanzu baitukan masu sanyaya zuciya na Hamisu Breaker ko M. Shareef sune ke debewa ‘yan mata da samari kewa.
Kowanne masoyi yana son jin kalamai masu sanyaya zuciya daga masoyinsa, wanda ke nuna an damu da shi kuma ana tunanin sa a ko da yaushe. Binciken lafiyar mutum da neman sanin halin da yake cikiy ana da muhimmanci sosai wajen nuna soyayya.
Musbahu Muhammad Goron Dutse JiharKano:
Akwai Bambanci Sosai, saboda a baya mazanda matan suna da kunya sosai ko da za su fadawa junansu kalaman soyayya sai dai su rubuta a wasika ba kamar yanzu ba idonka cikin Idonta za ta fada ko za ka fada.
A baya ina sonki ko ina kaunarki shi ne makurar kalaman soyayya, Amma Yanzu ina sonki, ina kaunarki, nayi Missing dinki, ina son ki zama abokiyar rayuwata da sauransu.
Sosai ma kuwa suna da tasiri idan mutum ba ya yi wa budurwarsa irin wadannan kalaman akwai matsala. Kwarai kuwa ina ciki. Ina sonka, ina kaunarka, Abban Wane da sauransu.