Daya daga cikin fitattun jaruman finafinan hausa dake masana’antar kannywood HAUWA ABUBAKAR AYAWA wacce aka fi sani da AZIMA GIDAN BADAMASI jarumar da ta shafe tsahon shekaru a cikin masana’antar kuma ‘ya ga tsohuwar furodusa a cikin masana’antar ta kannywood, shafin Rumbun Nishadi ya yi cozali da ita inda ta bayyana wa masu karatu wasu batutuwa da suka shafi sana’arta ta fim har ma da wasu batutuwan da suka shafi rayuwarta. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
Da farko za ki fadawa masu karatu cikakken sunanki tare da dan takaitaccen tarihinki.
Sunana Hauwa’u Abubakar Ayawa wacce jama’a suka fi sani da Azima gidan badamasi. Ni haifaffiyar garin kaduna ce, a garin kaduna nake, nayi firamare dina a garin kaduna nayi sakandare dina a ‘GGSS Kwatarkwashi Jihar Zamfara bayan nan na dawo na yi ‘Join Computer’ daga nan na fara kwalliya ‘Makeup’, amma dai ban mayar da hankali a kai ba, daga nan dai yanzu na fito da ‘Fashion House’ wanda nake dinki ina sayar da kayan jakunkuna, takalma, Material, abubuwa dai daya shafi ‘Collection’.
- Za A Gudanar Da Taron Tallata Fim Din “Red Silk” A Moscow
- Kasafin Kudi Na Naira Tiriliyan 1.78 Na Abuja Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa
Idan na fahimce ki kina so ki ce bayan fim kina yin wata sana’ar kenan?
Eh! Ina da shagon kayana wanda nake sayar da leshi, atamfa, jaka, takalma, material, ina dinkawa in kana so, akwai hijabai zan iya ce miki kayan yara takalman yara komai dai ‘collection’ ne na ‘Ayawa Collection’s’ a nan garin kaduna.
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?
Kin san komai a rayuwa akwai abin da Allah ya tsara maka kuma duk abin da Allah ya tsara maka za ka ga sai ya tabbatu, ni dai farko mahaifiya ta zan iya ce miki tsohuwar furodusa ce ta taba ‘producing film’ a da’, Momi Jamila Haruna Allah ya ji kanta kawar ta ce tare suke tun muna yara ba mu san za mu shiga harkar ba, har muka shiga harkar.
Ya gwagwarmayar shiga cikin masana’antar ta kasance?
Eh! to, kin san ita rayuwa ba za ka ce baka samu irin akasi ko damuwa da wannan ba, amma ni dai gaskiya zan iya ce miki Alhamdulillahi ni dai ina zaune da kowa lafiya kuma ban taba samun matsala da kowa ba, kuma za ki ga ni ban cika yawan yin fina-finani ba to, duk wanda nake haduwa da su a ‘location’ ne in kin ganni da jarumi ko jaruma to gaskiya a lokeshan ne to, kin ga indai ba a haduwar nan, matsala ba zai shigo ba, daman haduwa iya ta kwana biyu ko uku ce a rabu cikin dariya shikkenan. Sai na ce miki iya gidan badamasi ne ma muke kaiwa wata daya wata biyu to, shi ma kowa dakin shi daban in mun dawo gurin aiki da dare dakinka za ka shige to sai gobe in an hadu.
Ya batun iyaye lokacin da ki ka je musu da maganar kina son shiga harkar fim shin kin samu wani kalubale daga gare su ko kuwa?
A’a! ban samu ba kamar yadda na fada a baya mahaifiyata tsohuwar furodusa ce, ko da na je mata da maganar ban samu wata matsala ba abu daya ta ce mun ba ita kadai take da ni ba, in je in samu mahaifina duk abin da ya ce, ranar da na je na samu mahaifina ba zan manta da wata magana da yayi mun ba na ji dadinta ya ce; karatu fa? na ce zan ci gaba, aure fa? na ce baba, ya ce lokaci ne ko? A sa dai niyya, na yi dariya na ce in Allah ya yarda baba ku yi ta yi mana addu’a, Allah ya kawo mana mazaje nagari, ya ce Amin. Sannan ya ce Momi, na ce na’am, kina so? sau uku yana tambaya na ce eh, ya ce ubangiji Allah ya sa haka shi ne mafi alkhairi, ina yi miki fatan alkhairi, Allah ya kula da ke ya kare ki a cikin wannan masana’antar da za ki shiga, na ce masa amin.
Lokacin da ki ka fara shiga cikin masana’antar kannywood, da wacce jaruma ki ka fara cin karo da ita kuma wace ce babbar kawar ki cikin masana’antar?
Jarumar da muka fara haduwa da ita Anti Jamila Nagudu muka yi aiki da ita, a Kano da yallabai Ali Nuhu, su muka fara haduwa da su, ni ai dukka ‘yan’uwana ne ‘yan kannywood an zama daya tunda ina harkar, sun fi kawaye ‘yan’uwana ne kuma ana zumunci cikin ikon Allah.
Ya farkon fara fim dinki ya kasance?
Alhamdulillah zan iya ce miki ban samu wani firgici ko tsoro ba saboda ina son abun, na sa rai dole ina so, ko me aka ce na yi indai ba zai sabawa mutuncina, addinina, al’ada ta, to zan yi shi komene ne zan tsaya na jajirce na tsaya nayi shi ‘perfect’ yadda ake so. Wannan ma ba zan taba mantawa ba Mustapha M. Sharif shi ya fara daraktin dina a duniyar kannywood saboda wani abu ma dana yi farkon fim dina ‘Mussaffir’ shi na fara wani abu daya burge shi tsayawa ya yi cak, ya ce fim dinki nawa? na ce ban taba fim ba, ya ce ‘are you serious?’ na ce wallahi ban taba fim ba yaya, ya kira Obi bai yarda ba shi ne fim dina na farko, wannan yarinyar wace ce? a nan kaduna aka ce sunanta Hauwa Ayawa, ba ta taba yin fim ba? aka ce ba ta taba ba, ya ce Wow! abun ya burge shi ya ce gaskiya a je a siyo mata ‘sweet’ aka siyon sweet me tsinke na sha muka ci gaba da aiki.
Bayan fim din ki na farko ya fita ya ki ka ji a wannan lokacin, kuma wane irin kallo sauran al’umma suka rika yi miki kamar mutanen unguwa, kawaye, har ma da ‘yan’uwa?
Eh! ‘yar’uwa kin san ba za a rasa ba fa, maganganu gaskiya za a yi shi ana ma kan yin shi, amma ni dai abun da na sa a rai tunda na san sana’a ce kuma tsakani ga Allah zan yi kuma in Allah ya yarda ina kokari bari in yi abin da ba zai bata addinina ba kuma ba zan janyo wa iyayena magana ba, ba zan zubar da mutunci na ba, mutuncin gidanmu, ina ganin ko da na ji maganganun dai abin dole ya dame ka, amma na toshe kunne na rufe idanu tunda ni na san da yardar iyayena nake yi abin da in na tuna nake jin dadi kenan. Ina magana da zuciya ta da kaina “Ai Hauwa’u iyayena fa sun bar ni to me zai dame ni kuma daman albarkarsu nake nema to, me ya faru? kawai dai ki ci gaba da abin da ki ke, kin san daman dole mutum tara yake bai cika goma ba, in wani ya yabe ka dole wani ya bace ka, ko kuma wani na sonka dole wani ka ga akasin haka” to, amma fa maganganu an yi mun ji shi, amma cikin ikon Allah ga shi komai ya wuce, muna cikin alkhairi sai godiya ga ubangiji da kuma muna rokon Allah ya nunnunka mana ni’imominsa a gare mu.
Daga lokacin da ki ka fara fim kawo yanzu za ki yi kamar shekara nawa?
Gaskiya ‘yar’uwa in na ce miki ga ‘time’ din dana fara fim a yanzu gaskiya zan yi karya, ba zan iya tunawa da lokacin dana fara fim ba gaskiya.
Ko za ki iya tuna adadin finafinan da ki ka yi?
Na yi finafinai da dan dama, duk da wasu da yawa basu fito ba, dan wanda basu fito ba sun fi wanda suka fito yawa gaskiya, sai dai nayi finafinai cikin ikon Allah, gidan badamasi da sunan kin san yanzu ake kira na, yanzu na tashi daga Hauwa na koma Azima, ko ‘yan’uwa, kawaye, kowa Azima, ni yaushe ne ma nake cewa da Mamana “ni fa a yankan rago a dawo mun da sunana Azima” ina dariya, ta ce “Hauwa’un ne bakya so?” na ce ina son Hauwa’u amma mutane fa yanzu sun canza mun suna Azima Azima. Gaskiya akwai finafinai amma ba zan iya kayyade yawansu ba.
Wane fim ki ka fi so a cikin finafinan da ki ka fito ciki, kuma me ya sa?
Gaskiya fim din da ki ka ga na fito ina son shi duk finafinan da ki ka ganni ciki wanda ni nayi kowane irin fim ne gaskiya ina son shi kuma ina alfahari da wannan fim din.
Ko akwai wani waje cikin fim ko kuma shi kansa fim din da ki ka yi daga baya ki ka rika da-kin-sanin yinsa, idan akwai me ya sa?
Gaskiya babu ‘yar’uwa.
Ko akwai kalubalen da ki ka taba fuskanta bayan shigar ki cikin masana’antar?
Ah! akwai sosai ‘yar’uwa amma ba abin da zan ce sai dai na ce na barwa Allah komai, Allah shi ya san daidai, Allah kai mana kawai, amma akwai fa gaskiya.
Za mu ci gaba a makon mai zuwa
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp