Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce bai taɓa karɓar cin hanci daga hannun wani ɗan kwangila ko amfanin da kuɗaɗen ƙananan hukumomi ba tsawon shekaru takwas da ya yi a kan mulki.
Tsohon gwamnan ya ci gaba da cewa cikin shekaru 44 da ya yi yana rike muƙaman gwamnati, bai taɓa tattaunawa da wani ɗan kwangila don ya bashi kaso daga aikin da ya basa ba.
- AU Ta Naɗa Pantami Shugaban Tsara Manufofin Masana’antun Afrika Karo Na 4
- ‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Uwan Da Suka Birne Matashi Da Ransa A Kaduna
Kuma zai yi alfahari da cewa duk da ba shi kaɗai ba ne ke da wannan ɗabi’ar amma yana daga a cikin masu hakan.
Shekarau, wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar dalibai Musulmi ta Nijeriya, ya bayyana hakan ne a Abuja, yayin bikin cika shekaru 70 na ƙungiyar. Ya ce MSSN za ta ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa al’ummar Musulmi ta fuskar ilimi da tattalin arziki da siyasa.
A cewarsa, za a cimma hakan ne ta hanyar ayyuka iri-iri a makarantu da sauran al’umma tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyi masu ra’ayi iri ɗaya.
Ya ƙara da cewa za su yi ƙoƙarin ɓullo da sabbin tsare-tsare da za su ƙarfafa haɗin kai da ‘yan uwantaka da kuma kira ga ‘yan uwa su shiga harkokin siyasa da shugabanci.