Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce, babu nadama ko da na sani kan umarnin da ya bayar na rushe wasu gine-gine a sassan Jihar.
Gwamnan Yusuf ya bayyana hakan ne a lokacin da ya amshi bakwancin Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a gidan gwamnati da ya kawo masa ziyarar barka da babban Sallar Idi.
- Bikin Baje Kolin Cinikayya Ta Zama Dandalin Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
- Gwamnatin Sakkwato Ta Fara Biyan Alawus Din Masu Bukata Ta Musamman
“Mai martaba yana da kyau masarauta ta san cewa mun dukufa wajen aikin rusau ne domin dawo da wuraren al’umma da wasu suka mallaka ta hanyoyin da ba su dace ba. Za mu tabbatar dukkanin kadarorin jama’a an kwato su domin ci gaban al’ummar Jihar Kano.
“Babu nadama ko da na sani kan rusa wasu gine-ginen da gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje ta sayar.”
Gwamnan ya nemi hadin kan sarakunan gargajiya kan ayyukan da ya sanya gaba.
Ya gode wa sarkin da majalisar masarautar bisa kawo masa ziyara irinta ta farko tun bayan zamansa gwamna.
Kazalika, Abba ya bayyana wasu nasarorin da ya cimma cikin kwanaki 30 a matsayin gwamnan jihar.
Wasu daga cikin nasarorin da ya jero sun hada da biyan kudin jarabawar NECO ga daliban sakandare 55,000, farfado da hasken fitulun kan titi; rage yawaitar kwacen waya a birnin Kano.
Gwamnan ya roki sarakunan da su mara wa gwamnatinsa baya domin samun nasarar gudanar da tsare-tsare da manufofin kyautata mulki..
A bangarensa, Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ce sun kawo ziyarar ne domin gaisuwar sallah.
Ya bada tabbacin cewa za su ci gaba da bayar da shawarwarin da za su taimaka wajen gudanar da kyawawan ayyukan bunkasa jihar.
Sarkin ya nemi gwamnatin jihar da da masu ruwa da tsaki da tallafa wa masu karamin karfi duba da halin da ake ciki.