Yayin da take tsokaci game da hadin gwiwar Sin da Afirka a shekarar 2025, a gun taron manema labarai na yau da kullum da aka gudanar jiya Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta bayyana cewa, bangaren Sin na fatan habaka ma’anar al’umma mai makomar bai daya ta Sin da Afirka a sabon zamani tare da kasashen Afirka, da kuma kiyaye moriyar kasashe masu tasowa, da adalcin kasa da kasa, ta yadda za a inganta zaman lafiya da ci gaban duniya.
Mao Ning ta kara da cewa, a shekarar 2024, baki daga Sin da na kasashen waje su kusan 6,000, da suka hada da shugabannin kasashen Afirka 53 da suka kulla huldar diflomassiya tare da Sin, da shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka wato AU, da babban sakataren MDD, sun halarci taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a birnin Beijing, inda aka daga dangantakar Sin da dukkanin kasashen Afirka da suka kulla huldar diflomassiya da kasar, zuwa dangantaka bisa manyan tsare-tsare, kana an daga dangantakar Sin da kasashen Afirka gaba daya, zuwa ta al’umma mai makomar bai daya ta Sin da Afirka a sabon zamani.
Bugu da kari, yayin taron kolin Beijing na dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, an sanar cewa, Sin da kasashen Afirka za su inganta matakai guda 6, da ayyuka guda 10 don cimma zamanantarwa, kuma an gudanar da ayyuka masu inganci da yawa a kasashen Afirka. A sa’i daya kuma, kasashe masu tasowa da suka hada da Sin, da kasashen Afirka, sun zama babban karfi a duniya. Kana an zartas da sanarwar Beijing a gun taron kolin na Beijing, wadda ta fitar da muryoyin adalci na nuna adawa da ra’ayin fin karfi, da nufin rura wutar fito-na-fito tsakanin sassa daban daban, da neman raba-gari da sauran kasashe. (Safiyah Ma)