An wayi gari da kaɗuwa da samun labarin ruftawar wani bango a gidan wani magidanci mai suna Muhammad Sani Garba Dankama, inda mutum 6 suka rasa ransa, wasu kuma suna asibiti.
A daren Litinin bayan ɗaukewa ruwan sama, bango ya fada wa wata uwa da ‘ya’yanta guda biyar, inda nan take mutane 6 suka rigamu gidan gaskiya.
- Uwargidar Gwamnan Katsina Ta Nemi A Taimaka Wa Mata Wajen Yaƙi Da Ciwon Nono Da Na Mahaifa
- Gwamnatin Katsina Ta Gabatar Da Matsayarta A Taron Jin Ra’ayiyin Jama’a
Kamar yadda mahaifin yaran, Muhammad Sani Garba Dankama ya tabbatar wa manema labarai cewa bayan an kammala ruwan sama da misalin ƙarfe 2:00 na dare al’amari ya faru a unguwar Ƙofar Yamma cikin garin Dankama da ke ƙaramar hukumar Kaita ta Jihar Katsina.
Muhammad ya ƙara da cewa, baya gidan lokacin da lamari ya faru, inda ya ƙara da cewa lokacin da ya ji labarin bai san inda kaisa yake ba.
“Wannan al’amari ya faru ne da kusan mutum goma, amma dai mutum shida Allah ya yi musu rasuwa bayan faruwar lamarin, yanzu haka mutune uku suna asibiti suna karɓar magani,” in ji shi.
A cewarsa, daga cikin waɗanda Allah ya yi wa rasuwa akwai mahaifiyar yaran wato Mariya Sani, ‘yar shekara 45 da kuma Mujahid Sani, ɗan shekaru 20, sai Zahariya Sani, ‘yar shekara 18.
Sauran sun haɗa da Hauwa Sani, ‘yar shekara 15 da Amira Sani, ‘yar shekara 3 da kuma Nura Sani, ɗan shekara 5.
Muhammad ya bayyana cewa yanzu haka akwai waɗanda suka samu raunuka, inda suke asibitin Katsina domin karɓar magunguna.
Mahaifin yaran ya bayyana irin kaɗuwar da ya yi lokacin da ya samu labarin faruwar wannan al’amari, wanda ya ce ya yi wa Allah godiya, su kuma da suka rasu Allah ya jikansu.
Yanzu haka dai ‘yan’uwa da abokan arziki na ci gaba da zuwa yi wa Malam Muhammadu ta’aziyyar rasuwar iyalansa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp