Bankin TAJ ya sake lashe kyautar gwarzon bankin Musulunci na 2023, wanda jaridar Business Day ta ba shi wanda ya doke sauran bankuna har karo na uku.
Da yake mika lambar yabo ga mahukuntan bankin wanda shugaban sashe na Jihar Legas, Michael Iteye ya wakilce shi a yayin bikin bayar da kyautuka na bankin na jaridar da aka gudanar a Legas, wakilin Jaridar Business Day ya bayyana cewa an ba da lambar yabon ne ga bankin TAJ bisa la’akari da jajircewa wajen gudanar da ayyukansa duk da irin kalubalen harkokin kudade da ake fama da shi a Nijeriya.
- Mutum 2 Sun Shiga Hannu Kan Fashin Katin ATM A Kaduna
- CBN Ya Rufe Wasu Bankuna 754 Sakamakon Shiga Matsaloli
Da yake amsar lambar yabon daga jaridar, shugaban bankin, Hamid Joda, ya ce, “Kamar yadda ake cewa, aiki tukuru yana bayar da cikakken sakamako. Don haka, lambar yabon da bankin Musulunci da muka samu daga Business Day na bana, ya nuna cewa mutane suna sane da irin ayyuka tukuru ta muke gudanarwa domin faranta wa abokan huldarmu.
“Muna farin ciki da wannan karramawa, wannan lambar yabo ya zo ne bayan wata hudu da TAJBank ya zama na daya a cikin bankunan da ke bayar da bashi babu kudin ruwa samun riba a hada-hadar hannun jarin Nijeriya na 2023.
“Kamar yadda muka fada daga farko, samun gamsuwar abokan hulda shi ne namu”.
Idan za a iya tunawa dai bankin TAJ ya lashe kyautar jaridan Business Day a 2021 da 2022, kafin wannan ma ya lashe lambar yabo ta gwarzar bankin shekarar 2020 da kamfanin LEADERSHIP ya ba shi.