A yayin da shekara ta 2023 ke bankwana a wannan makon, Kamfanin Jaridar LEADERSHIP HAUSA ya zakulo wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a wannan shekarar ta 2023 a bangaren wasanni.
Wasu daga cikin abubuwan da suka faru a bangaren wasanni a shekara mai karewa shi ne a ranar Laraba 6 ga watan Yuli na shekara ta 2023 aka kece-raini a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da takwararta ta Katsina United a wasan raba-gardama na neman tsallakewa zuwa gasar Firimiyar Nijeriya na kungiyoyi 8 da ke kira Super 8, inda a ciki za a dauki kungiyoyi hudu, biyu a Arewa, biyu a Kudu su dawo gasar Firimiyar.
- Gwamnan Katsina Ya Yi Wa Ma’aikatan Jihar Ƙarin ₦10,000 Kan Albashi, ‘Yan Fansho ₦5,000
- INEC Ta Tilasta Wa Daraktocinta 4 Yin Ritaya
A wasan karshe, Katsina United ta doke Kano Pillars da ci daya mai ban-haushi, inda Bictor Mbaoma ya zura kwallo a ragar Kano Pillars a bugun finareti, sai dai duk da an doke Pillars, kasancewar kungiyar DMD ta doke kungiyar EFCC ta Abuja, sai kungiyoyin Katsina United da Kano Pillars suka samu nasarar tsallakawa zuwa Firimiya.
DMD ta lallasa EFCC da ci 3-0, inda Kano Pillars ta kare da maki shida, Katsina United ta samu maki shida, DMD da EFCC suka samu maki uku-uku. A kakar bara ce dai kungiyar ta Kano Pillars ta yi rashin nasara, inda ta koma rukuni na biyu na gajiyayyu a gasar Nijeriya kuma a tarihin Kano Pillars, wadda aka kafa a 1990, sau uku tana buga gasar rukuni na biyu a 1994 da 1999 da kuma bana.
Daga cikin dalilan da suka jawo faduwar Pillars, akwai samunta da laifi da hukumar shirya gasar ta yi bayan ta dawo buga wasa a filin wasa na Sani Abacha, inda aka mayar da Pillars din Kaduna da buga wasannin gida.
A wasan da aka buga na Arewa mafi zafi wato Northern Derby da Katsina United ce aka samu rikici, inda magoya bayan Pillars suka farfasa motar Katsina United haka kuma a wasan da aka buga tsakanin Kano Pillars da Dakkada FC, shugaban kungiyar Kano Pillars na lokacin, Surajo Shu’aibu Yahaya wanda aka fi sani da Jambul ya yi wani laifin, inda aka sake kwashe wa Pillars maki uku, ya kama maki shida kenan.
Sai dai ba don cire maki shidan ba, da kungiyar ba ta koma baya ba kuma a lokacin Pillars ta daukaka kara domin a dawo mata da makinta, amma ba ta samu nasara ba.
A daya bangaren, kungiyar Sporting Lagos ce ta bayar da mamaki, inda ta samu nasarar zuwa gasar Firimiya a shekara biyu kacal da kafuwarta inda kungiyar ta doke Stormers da ci 2-0, inda nan take ta samu tsallakawa zuwa Firimiyar.
An kafa kungiyar ne a shekarar 2022 a Legas, sai dai tana da karfin dukiya, inda a watan Maris na bana ta shiga kwantiragi da kulob din Aarhus Fremad da ke kasar Denmark, sannan ta shiga yarjejeniyar buga rigunan wasa da Kamfanin Klasha.
Shugaban kungiyar, Godwin Enakhena ne ya jagoranci kungiyar MFM lokacin da ya dago ta zuwa gasar Firimiya, kamar yadda ya yi da Sporting Lagos a yanzu sannan a lokacin hada wannan rahoto, ba a kammala daya wasann Kudu ba, inda za a samu kungiyar da za ta hadu da Sporting Lagos wajen tsallakowa gasar Firimiyar da kungiyar Heartland.
- Osimhen Ya Zama Gwarzon Dan Wasan Afirka
Sannan a ranar 11 ga watan Disamba na shekarar 2023 dan wasan tawagar Nijeriya, Bictor Osimhen ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafar Afirka na shekarar 2023.
Dan wasan na Super Eagles ya lashe kyautar a bikin da aka gudanar a Marrakech, wanda ya ja ragamar kungiyar kwallon kafa ta Napoli ta lashe Serie A karon farko bayan shekara 33.
Osimhen ya yi takara tare da dan wasan Morocco Achraf Hakimi da na Masar Mohamed Salah kuma gaba daya ya doke su ya lashe wannan kyautar wadda rabon da dan Nijeriya ta lashe shekara 33 kenan.
Dan wasan shi ne ya kai Super Eagles gasar kofin Afirka da za a yi a Ibory Coast a farkon wannan shekarar, wanda ya ci kwallo 10 a karawar cancantar shiga gasar cin kofin.
Osimhen ya ci kwallo 27 a dukkan fafatawa a Napoli, wadda ta koma kan ganiya a kwallon Italiya a kakar wasa ta 2022 zuwa 2023, sannan dan wasan mai shekara 24 ya zama na farko a Napoli da ya zama kan gaba a cin kwallaye a babbar gasar kwallon kafar kasar ta Italiya tun bayan Diego Maradona a 1987 zuwa 1988, sannan Osimhen ya zama dan Nijeriya na farko da ya lashe kyautar tun bayan Kanu Nwankwo a 1999.
A fannin mata Asisat Oshoala (Nijeriya, Barcelona) ita ce ta lashe gwarzuwar kwallon kafa ta Afirka ta 20223, sannan ta kuma yi takara tare da Thembi Kgatlana (Afirka ta Kudu, Racing Louisbille) da kuma Barbara Banda (Zambia, Shanghai Shengli).