A yau Litinin ne Shugaba Buhari zai yi wata ganawar gaggawa da manyan shugabannin tsaron kasar nan a babban birnin tarayyar Abuja, musamman domin sake yin nazari wajen kara karfafa lamarin harkar tsaro.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban kasar ya fitar, Malam Garba Shehu a babban birnin tarayya, Abuja.
A cewar sanarwar, shugaba Buhari wanda a farko aka tsara zai tafi kaddamar da hukumar (NASENI) zai gana ne da manyan shugabannin tsaron kasar domin kara yin dubi kan sauran matakan da ya kamata a dauka don a kara karfafa lamarin harkar tsaro na kasar Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp