- Ta’adin Da Aka Yi Daga 2019 Zuwa 2022
- ‘Yan Nijeriya Ku Taimaka Mana – Hukumar
- Komai Runtsi Dole A Yi Zabe – Shugabannin Addini
- Ba Zan Bari A Yi Magudi Ba – Buhari
Sakamakon barazanar yawaitar kone-konen ofisoshin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) musamman a sashen kudancin kasar nan, hukumar ta fito fili ta nemi taimakon ‘Yan Nijeriya a kan su nuna kishin kasa wajen kare mata ofisoshin nata daga mabarnata, wanda ta ce zafafan hare-haren da ake kai wa ofososhin munakisa ce ga zaben 2023.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi rokon haka a yayin ganawa da dattawan kungiyar bunkasa tattalin arzikin yammacin Afirka (ECOWAS) wanda ya gudana a shalkwatar INEC da ke Abuja.
Tawagar da tsohon shugaban kasar Sierra Leone, Ernest Bai Koroma da tsohon mataimakin shugaban kasar Gambiya Fatoumata Jallow-Tambajang suka jagoranta.
INEC ta ce a cikin watanni hudu kacal an kona mata ofisoshi akalla guda bakwai baya na baya da aka yi.
“Muna tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za mu mayar da hankali ga gudanar da zabe, dole ne mu roki ‘yan kasa su taimaka mana su sa ido kan kayayyakinmu a dukkan fadin Nijeriya.
“Nauyi ne da ya rataya a wuyanmu wajen hada kai domin tsare kayayyakin. Dole ne a dakatar da farmakin, sannan a damke wadanda suke da hannu tare da hukunta su.” In ji shi.
A cikin makonni uku da suka gabata, ‘yan ta’adda sun kona ofisoshin INEC guda uku a jihohin Ogun, Osun da kuma Ebonyi. Haka kuma a cikin wata hudu, sun banka wuta a wasu ofisoshin hukumar guda bakwai a Jihar Imo.
Yayin da farmakin jihohin Ogun da Osun suka fara a ranar 10 ga Nuwambar 2022, an kai farmaki a jihohin Ebonyi da Imo a ranar 26 ga watan Nuwamba zuwa ranar 1 ga Disamba. Wannan alkaluman farmakin da aka lissafo sun yi sanadiyyar rasa muhimman kayayyaki da za a yi amfani da su a babban zaben 2023.
A Jihar Ogun, an dai kone akwatunan zabe guda 904 da katukan jefa kuri’a wadanda ba a amsa ba guda 65,699 da rumfunan zabe 29 da jakunkunan zabe 57 da kuma janareta guda uku.
A karamar hukumar Izzi da ke Jihar Ebonyi, kuwa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safe, inda aka babbake ginin ofishin da dukkan kayayyakin da ke ciki kurmus. A cewar mai magana da yawun INEC, Festus Okoye kayayyakin da suka kone sun hada da akwatunan zabe guda 340 da kananan rumfunan zabe 130 da janareta 14 da mayan tankokin ruwa da kujeru da katunan jefa kuri’a wanda har yanzu ba a san adadinsu ba.
Duk da wadannan zafafan hare-haren, INEC ta sha alwashin gudanar da sahihin zabe a 2023. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ya tabbatar wa da ‘Yan Nijeriya har ma da sauran duniya hakan a yayin da yake wani jawabi a Jihar Ogun da kuma lokacin da ya karbi bakuncin tawagar wakilan Kungiyar Hadin Kan Afirka a Abuja. Ya ce hukumar za ta mayar da dukkan kayayyakin da ta rasa lokacin wannan farmaki.
“A wadannan farmaki guda uku, ba a samu rasa rai ba, amma an samu asarar kayayyakin zaben 2023 masu yawa. Abun ban sha’awa dai shi ne, za mu iya dawo da dukkan kayayyakin da muka rasa, amma kuma ya kamata a dakatar da faruwar lamarin.
“Za mu ci gaba da hada kai da jami’an tsaro domin karfafa tsaro a dukkan ofisoshinmu, jami’anmu da kuma kayayyakin zaben 2023. Muna damuwa kan farmakin da ake kai wa a ofisoshinmu, amma hakan ba zai taba hana zaben 2023 ba.
A yake jinjina a cikin jawabinsa, Babban mashawarcin gudanarwa na UNDP, Mista Deryck Fritz ya bayyana cewa mika ragamar shugabancin cikin kwanciyar hankali da lumana ya ta’allaka ne da kyakkyawan zabe da ‘yan siyasa da kungiyoyin fararen hula da sauran al’umma suka aminta da shi.
Kone-konen ofisoshin INEC na baya-bayan nan ba su ne somau ba, domin ko a 2019, ‘yan ta’adda sun banka wa ofisoshin INEC wuta a jihohin Abiya, Filato, Ribas, Anambra, Osun, Akwa Ibom da kuma Jigawa.
Haka nan, idan za a iya tunawa a ranar 12 ga watan Fabrairun 2019, ‘yan ta’adda sun kone shalkwatar INEC da ke Awka a Jihar Anambra kurmus inda aka yi asarar na’urar zabe guda 4,695 da sauran muhimman kayayyakin zabe.
A 2020, an samu irin wannan lamari har guda hudu a jihohin Anambra, Imo, Abuja da kuma Ondo.
Haka kuma a 2021, an kai irin wadannan farmaki a ofisoshin INEC da ke jihohin Akwa Ibom da kuma Abiya. Haka nan a jihohin Ebonyi da kuma Inugu. A ranar 2 ga watan Mayun 2021, an kai hari kan ofishin INEC da ke karamar hukumar Essien a Jiohar Akwa Ibom, inda aka kone akwatunan zabe guda 345 kanakan rumfunan zabe 135 da wayoyin hannu da tankokin ruwa da kayayyakin kujeru.
A 2022 kuwa, abin ya fantsama har zuwa Jihar Zamfara, kodayake rahotanni sun tabbatar da cewa ba hari ne aka kai wa ofishin na INEC a Kauran Nomada ba illa gobara ce ta tashi wadda ‘yansanda ke binciken musabbabinta.
Abun damuwar dai shi ne, dimbin asarar da hukumar ke yi, wanda hakan ya sa, Babban Sufetan ‘yansanda, Usman Baba Alkali zai gana da shugabannin jam’iyyun siyasa a shalkwatar rundunar ‘yansanda da ke Abuja a makonni masu zuwa. Har ila yau, wakilin INEC da darakta janar na hukumar bayanan sirri ta kasa, Ahmed Abubakar da babban jami’an tsaron sirri na sojoji, Manjo Janar Samuel Adebayo da wakilan jami’an ‘yansandan sirri (DSS) da sauran hukumomi za su halarci taron.
Babban Sufeton ‘yansanda ya ce a wani mataki na rigakafi, gwamnatin ta jibje jami’an sojoji da na DSS da jami’an NSCDC da kuma jami’an kashe gobara a dukkan ofisoshin INEC da ke fadin kasar nan.
Ya kara da cewa an umurci jami’an tsaro su gudanar da binciken sirri kan wadanda suke aikata lamarin da kuma laifuffukan zabe da ake tafkawa a yanzu haka.
INEC ta gano an tafka laifukan zabe har guda 52 da suka danganci kalaman batanci da zage-zage da farmaki karara ga abokan adawa tun daga lokacin da aka fara yakin neman zaben 2023, ranar 28 ga watan Satumba.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu wanda ya bayyana hakan, har ila yau ya ce an kuma samu ci gaba, yayin da ‘yan siyasa suke ziyartar wuraren da ba su taba kai ziyara ba domin gudaar da yakin neman zabe.
Haka kuma Yakubu ya yi kira ga majalisa ta kara kaimi wajen amincewa da kudirin dokar kafa hukumar hukunta masu karya dokokin zabe.
Komai Runtsi Dole A Yi Zabe – Shugabannin Addini
A halin da ake ciki kuma, Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar hadaka ta addinan Nijeriya (NIREC), Alhaji Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa komin runtsi dole a yi zaben 2023 duk da tsananin farmaki da ake kai wa ofisoshin hukumar INEC.
Ya bayyana hakan ne a Abuja lokacin taron NIREC karo na hudu da aka yi wa taken ‘Samun sahihin zabe a kasa shi ne tafarkin farfadowa’.
A cewarsa, Shugaba Buhari ya sha alwashin gudanar da sahihin zabe a 2023, duk wanda ya yi kokarin wargaza kokarinsa, to ya kamata a dauki mataki a kansa.
“Kafin gudanar da zabe, muna samun damar ganawa da shugabannin tsaro domin tattauna da su kan yadda mutane suke jin tsoro dangane da zabe. mafi yawan mutane sun bayyana ra’ayoyinsu game da zaben 2023 kan ko zai yuwu ko kuma akasin haka, sai dai ni na tabbatar da zai yuwu. Ni ban yarda da abin da suke fadi ba. Zabe ne wanda mutane za su jefa kuri’arsu cikin kunciyar hankali, sannan duk wanda Allah ya ba shi nasara to shi zai shugabanci kasar nan da kuma gwamnoni a jihohin da muka fito.
“Kar mu sake mu amince da mutanen da suke daukan zabe ko a mutu ko a yi rai. Mu fita mu gudanar da kamfen cikin kwanciyar hankali. Kowacce kasa tana da irin nata matsalolin da take fuskanta. A shekarar da ta gabata, wani abu ya faru a kasar Amurka, inda shugaban kasa da ke kan mulki ya rasa kujeransa. Haka ma sauran kasashen Turai suna da irin nasu matsalolin.
“Kar mu dunga kallon kasashen Turai ko Amurka ko kuma sauran kasashe. Ya kamata mu dunga kallon matsalolinmu da yadda za mu iya warware su. Kwanaki 10 da suka ganata ina Maiduguri, inda na gabatar da lacca kan shugabanci da kuma matsalolin da muka fuskanta. Su na nan a kafafen sadarwa. Na ce muna tunanin wadannan kasashe sun fi mu ne. Ko kadan ba su fi mu ba, sai dai muna bukatar tsari da zai sa ayyukanmu su fadada. Idan har ayyukanmu suka fadada, komi zai daidaita. Sun san abubuwan da muka da su. Allah ya albarkace mu da abubuwa masu yawan gaske. Likitoci nawa muke da su da ke aiki a kasashen ketare. Idan har aka canza tsari suka dawo Nijeriya komi namu zai daidaita.
“Zaben 2023 ya kasance sabon aiki ne wanda mutane za su jefa kuri’a, inda Allah da kuma INEC za su bayyana wanda ya yi nasara. Dole INEC ta shirya zabe, sannan dole jami’an tsaro su samar da tsaro. Jami’an INEC nawa aka kona? Wani rawa jami’an tsaro suke takawa? Wadannan su ne tambayoyin da ya kamata mu tambayi kawunanmu.
“Ba da jumawa ba shugaban kasa ya je Sakkwato, inda ya bayyana cewa yana kokari wajen gudanar da sahihin zabe. shugaban kasa da bakinsa ya fadi haka, saboda haka me zai sa wani ya saka shakku a cikin lamarin? Yana iya bakin kokarinsa kuma ina da tabbacin zai tsayu a kan kalamunsa. Idan har wasu na kokarin tarwatsa kokarinsa, a matsayinsa na shugaban askawan Nijeriya ya kamata ya dauki mataki. Domin haka, za mu yi aiki da abin da shugaban kasa yake kokarin samun nasarar kasar nan.”
Hakazalika a nasa bangaren, shugaban kungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN),
Archbishop Daniel C. Okoh, wanda yana daga cikin shugabannin NIREC, ya bayyana cewa a daidai lokacin da kasar nan ke fuskantar zaben 2023, an samu tambayoyi masu yawa da kuma shakku kan yadda Nijeriya za ta iya gudanar da sahihin zabe.
Ya ce, “Kasarmu za ta iya gudanar da sahihin zabe a 2023, amma wannan ya danganta ne da yadda muka yi aiki tare.
“Wannan taro yana da matukar muhimmanci ga mambobin NIREC wajen tattauna zaben kasarmu a 2023. Wannan shekara ce da muke jira domin samun sahihin zabe da zai ba mu damar zaben shugabannin siyasa da za su samar da sabuwar Nijeriya.
“Zabe wani tsari ne na dimokuradiyya da mafi yawancin kasashen duniya ke gudanarwa. Tsari ne da zai bai wa mutane damar zaben shugabannin.
“Ba na ko shakka a zuciyata cewa zaben 2023 zai gudana wanda zai bayar da ‘yanci samar da tsaro da bunkasa tattalin arziki da dai sauran dukkan bangarori.
“Ya zama wajibi a gudanar da sahihin zabe wanda dole mu shugabannin addini za mu bayar da gudummuwa wajen samun nasara. A wannan karon za mu yi amfani da kafafen sadarwarmu wajen kai sakonni na musamman na samun fatan zaman lafiya da halin kai da mutunta juna. Dole mu kalubalanci duk wani mataki da zai kawo matsaloli kan wannan lamari.
“A bangaren CAN, dole ne mu tsayu wajen gudanar da zabe. Tuni mun tsara masu saka ido kan zabe a manyan mazabu da ke sassa daban-daban na Nijeriya wadanda za su binciki yadda zaben 2023 ya gudana. Ya kamata mu yi aiki tare da sauran masu saka ido ciki har da na kasa da kasa da ke kawance da Nijeriya. Wannan ba sabon abu ba ne a wurinmu, domin mun gudanar da irin wannan lamari a zaben 2019. Mun wallafa binciken da muka yi ga ‘yan Nijeriya. Wannan shi ne babban abun da ya kamata mu yi a matsayinmu na kungiya da ke sha’awar zaman lafiya da gudanar da sahihin zabe,” in shi Okoh.
Ba Zan Bari A Yi Magudi Ba – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada cewa zaben 2023 zai kasance sahihi wanda ba zai bari a mured ba.
Shugaban kasa ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da dattawan kungiyan yammacin Afirka wanda tsohon shugaban kasar Sierra Leonean, Dakta Ernest Bai Koroma yake jagoranda a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
“Ina muku godiya a kan amincewa da yin wannan aiki na kungiyar yammacin Afirka, idan aka duba yadda muka gudanar da sahihin zabe a jihohin Anambra da Ekiti da Osun, domin haka gwamnatin tarayya za ta bari mutane su zabi shugabanni da kansu. A halin yanzu zai yi wahala a iya murde zabe,” in ji shi.