Kungiyar Likitocin Nijeriya (NARD) ta bayar da gargadi na kwanaki 10 ga Gwamnatin Tarayya da hukumomin da abin ya shafa don cika bukatun walwalar membobinta, tare da jan hankali cewa idan ba a dauki mataki ba kafin karewar wa’adin, za su tsunduma yajin aiki a fadin kasar.
A cikin wata sanarwa da shugaban NARD, Dr. Tope Osundara; Sakatare Janar, Dr. Oluwasola Odunbaku; da Sakatare na Harkokin Yada Labarai da Al’umma, Dr. Omoha Amobi, suka sanya wa hannu, likitocin sun ce wannan shawarar ta biyo bayan sakamakon zaman Gwamnatin Zartarwa ta Kasa na Musamman da aka gudanar ta Intanet a ranar Lahadi.
- Spence Na Dab Da Kafa Tarihin Zama Musulmi Na Farko Da Zai Buga Wa Ingila Ƙwallo
- Gwamnatin Kebbi Ta Ba da Ƙwangilar Gina Hanyoyi Kan Naira Biliyan 2.1
NARD ta tunatar da cewa a watan Yuli ta bayar da wa’adin makonni uku, amma “don amfanin zaman lafiya a aiki,” Kwamitin Zartarwar Kasa (NEC) ya tsawaita wa’adin da wasu makonni uku don bai wa Kwamitin Shugabannin Kasa damar tattaunawa da masu ruwa da tsaki.
Sanarwar ta ce, “E-NEC ta yi Allah-wadai da gazawar Gwamnatin Tarayya wajen cika alkawuranta, tare da nuna bakin ciki cewa babban adadin likitocin kasar ba a biya su ba don Asusun Horon Likitocin Kasar na shekarar 2025. Haka kuma, gwamnati ta ki biyan bashin watanni biyar da suka rage sakamakon sake duba tsarin albashin Likitocin Hadin Gwiwa na kashi 25/35, da sauran tsofaffin bashin albashi.”
“E-NEC ta nuna rashin jin dadinta kan dankwafe mutane ba bisa ka’ida ba na takardun membobinsu na Kwalejojin Likitoci da Masu Koyar da Lafiya na Yammacin Afirka (WACP/WACS) da Hukumar Likitocin Hakoran Nijeriya (MDCN) ta yi, da kuma ci gaba da rashin bayar da takardun mambobinsu daga Kwalejin Likitocin Kasa na Bayan Digiri (NPMCN).”
Kungiyar ta kara sukar gazawar biyan bashin Alawus na Kayan Aiki na shekarar 2024, tare da Allah-wadai da wasu gwamnatocin jihohi saboda watsi da likitocinsu.
“E-NEC ta yi Allah-wadai cikin da gazawar Gwamnatin Jihar Kaduna wajen cika alkawuran ta ga mambobi a karkashin ARD Kaduna da Asibitin Koyarwa na Barau Dikko, duk da yarjejeniyoyi da Fahimtar Juna da aka sanya hannu a baya. Haka kuma, E-NEC ta yi Allah-wadai da gazawar Gwamnatin Jihar Oyo wajen magance kalubalen da mambobin ARD Asibitin Koyarwa na LAUTECH, Ogbomosho ke fuskanta, duk da ci gaba da yajin aiki mara iyaka a asibitin,” in ji sanarwar.
Duk da haka, NARD ta yaba wa gwamnonin jihohi da suka riga suka biya Asusun Horon Likitocin Kasar na 2025 (MRTF), tare da nuna cewa irin wadannan matakai na nuna himma wajen kula da walwalar likitoci.
Sanarwar ta ce, “E-NEC ta yi Allah-wadai da gazawar Gwamnatin Tarayya wajen cika alkawuranta, tare da nuna bakin ciki cewa babban adadin likitocin kasar ba a biya su ba don Asusun Horon Likitocin Kasar na shekarar 2025. Haka kuma, gwamnati ta ki biyan bashin watanni biyar da suka rage sakamakon sake duba tsarin albashin Likitocin Hadin Gwiwa na kashi 25/35, da sauran tsoffin bashin albashi.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp