Kungiyar kwallon kafa ta Fc Barcelona tana kokarin dauko Victor Osimhen a matsayin wanda zai maye gurbin Robert Lewandowski, Osimhen yana cikin jadawalin ‘yan wasan da Barcelona ke nema a bana, an sha danganta dan wasan da komawa Catalonia a shekarar da ta gabata, don haka ba abin mamaki ba ne ganin sunansa ya sake bayyana a matsayin wanda zai maye gurbin Robert Lewandowski.
Dan jaridar kasar Sifaniya, Gabriel Sans na Mundo Deportivo ya bayyana cewar, Barcelona na neman wanda zai maye gurbin Robert Lewandowski a matsayin mai jefa kwallo a raga, ga abin da ya ce game da Osimhen da Barcelona, “Barcelona tana bukatar kwararren dan wasan gaba, kuma tana fatan samunsa a kakar wasa mai zuwa”, amma kuma zuwa yanzu ba a tabbatar ko Lewandowski zai ci gaba da zama a kungiyar ba.
Gabriel ya cigaba da cewa” sakamakon haka ne Barcelona ke fatan samun wani wanda zai maye gurbinsa haka yasa suka nemi Victor Osimhen, amma kuma zuwa yanzu babu tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, Osimhen na cikin jerin yan wasan da Barcelona za ta siya a bana, amma muna bukatar duba yanayin Lewandowski, ba mu san yadda makomarsa a kungiyar za ta kasance ba.
Matsalar, kamar ko yaushe, ita ce gaskiyar cewa Osimhen ba zai yi arha ba kuma Barcelona za ta yi fama da biyan manyan “yan wasa a bazara mai zuwa, Julian Alvarez da Erling Haaland sun riga sun kasance cikin wadanda kungiyar ta Catalonia ta fara nema, yayin da kuma ta ke kallon Etta Eyong da Serhou Guirassy na Borrusia Dortmund.
 
			




 
							








