Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta koma kan teburin gasar Laliga bayan doke Real Sociedad da ci 2-1 a wasan da suka buga ranar Lahadi. Joules Kounde da Robert Lewandowski ne suka zura ƙwallayen biyu da suka tabbatar da nasarar.
Da wannan sakamako, Barcelona ta tattara maki 19 daga wasanni bakwai, tana da tazarar maki daya da Real Madrid wadda ta sha kashi a hannun Atletico Madrid da ci 5-2 a ranar Asabar. Masu riƙe da kofin gasar, Barcelona, na fatan lashe Laliga karo na biyu a jere tun bayan shekarun 2017/2018 da 2018/2019.
- Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff
- Atletico Madrid Ta Zazzaga Wa Real Madrid Ƙwallaye 5 A Metropolitano
Haka kuma, dawowar matashin ɗan wasa Lamine Yamal daga jinya ta taimaka matuka, musamman yadda ya bayar da taimako a ƙwallo ta biyu da Lewandowski ya ci. Yamal, wanda aka karrama a kwanan nan da kyautar gwarzon matashin ɗan wasa a Ballon d’Or, ya samu gagarumar karɓuwa daga magoya bayan Barcelona.
Kocin ƙungiyar, Hansi Flick, ya yaba da jajircewar ƴan wasansa, inda ya buƙace su da su ƙara dagewa a sauran wasannin. Barcelona za ta fuskanci Paris Saint-Germain (PSG) a gasar Zakarun Turai ranar Laraba, kafin ta ziyarci Sevilla a gasar Laliga ranar 5 ga watan Oktoba.