Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta tube mai tsaron ragar kungiyar, Marc-Andre ter Stegen daga mukamin kaftin din kungiyar a wani mataki na hukunta dan wasan na kasar Jamus, an yi wa dan wasan mai shekaru 33 tiyata a baya a karshen watan Yuli, rahotanni sun bayyana cewa, rikicin da ke tsakaninsa da Barcelona ya samo asali ne sakamakon rashin bayyana asalin yanayin lafiyarsa ga hukumar Laliga, wanda hakan na iya bai wa kungiyar damar yin rijistar sabbin ‘yan wasa na tsawon lokacin da ba ya taka leda.
Kwanan nan, Ter Stegen ya wallafa wani rubutu a shafukansa na sada zumunta, ya na mai cewa zai yi jinyar watanni uku kacal, duk da cewar dokokin La Liga sun bukaci dan wasan ya yi jinya na akalla watanni hudu domin a dauke shi a matsayin wanda ba ya nan na dogon lokaci, zakarun na gasar La Liga na fatan yi wa sabbin yan wasanta Joan Garcia wanda yazo daga Espanyol da dan wasan Ingila Marcus Rashford da ya zo a matsayin aro daga Manchester United rajista.
- Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas
- Sojoji Sun Kama Mai Yi Wa Boko Haram Safarar Man Fetur A Borno
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Barcelona ta ce, “bayan kwamitin ladabtarwa da aka kafa akan mai tsaron ragar na kasar Jamus Marc-Andre ter Stegen, bisa yarjejeniya tare da jagorancin shugabannin wasanni da kuma masu horar da yan wasa, ta yanke shawarar tumbeke Stergen daga matsayinsa na kyaftin na wani dan lokaci”.
Sun kara da cewa,”A cikin wannan lokaci, mataimakin kyaftin na yanzu, Ronald Araujo ne zai karbi aikin kyaftin din, Ter Stegen ya buga wa Barcelona wasanni sama da 400 tun lokacin da ya koma kungiyar daga Borussia Monchengladbach a shekara ta 2014, ya lashe manyan kofuna da suka hada da gasar zakarun Turai da kuma gasar La Liga shida a kungiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp