Wani rahoto da ofishin kula da basuka da rance na Nijeriya (DMO), ya fitar, ya ce bashin da ake bin Nijeriya a karshen watan Yunin 2024, ya haura dalar biliyan 42.9, kwatankwacin naira tiriliyan 71,826,183,000,000.
Cikin basukan da ake bin Nijeriya, akwai na gwamnatin tarayya da ya kai dala biliyan 38, inda jihohi da babban birnin tarayya ake bin su bashin dala biliyan 4.89, wanda shi ma kwatankwacinsa ya kai naira tiriliyan 8,187,180,300,000. Sannan akwai wasu basukan cikin gida da ake bin jihohi da ya kai naira tiriliyan 4.27.
- Messi, Ronaldo, Lookman Na Cikin ‘Yan Wasan Da Ke Takarar Kyautar Globe Soccer Awards Ta Bana
- Salon Zamanantarwa Irin Na Kasar Sin Riba Ce Ga Duniya Baki Daya
Cikin basukan dai akwai na Bankin Duniya da kuma Asusun bada Lamuni (IMF) da suka kai dala biliyan 17.13, sai kuma na Tarayyar Turai da ya kai dala biliyan 15.12.
Sauran daidaikun kasashen duniya da kuma bankuna su kuma suna bin Nijeriya bashin dala biliyan 5.49.
A bashin da ake bin jihohin Nijeriya, Jihar Legas ce ke kan gaba, inda kudin da ake binta ya haura dala biliyan 1.2, sai kuma Jihar Kaduna da ke biye ta mata da bashin dala miliyan 640.99.
Daga cikin basukan gida da ake bin jihohin, Legas ce ke kan gaba inda ake bin ta bashin naira biliyan 885.99, sai kuma Jihar Ribas da ake bi bashin naira biliyan 389.2.
Sai dai Nijeriya ta kashe dala biliyan 10 a shekarar 2023 wajen shigowa da kayan abinci, kamar yadda a Bankin Raya Nahiyar Afirka (AfDB), wanda masana ke ganin wani babban gibi ne da ke kassara tattalin arzikin kasar, idan aka kwatanta yadda kasar ke da dimbin arzikin albarkatun noma.