Kakakin ma’aikatar rundunar sojin kasar Sin Zhang Xiaogang, a yau Laraba ya yi Allah wadai da rahoton tantance barazana da Amurka ta fitar, wanda ke kunshe da kalaman rashin da’a da ta yi kan kasar Sin, yana mai cewa shafawa kasar Sin kashin kaji ba zai tamaika kawar da tambarin Amurka a matsayin daular kutsen intanet ba.
Kakakin ya bayyana hakan ne yayin da yake bayar da amsa ga taron manema labarai dangane da rahoton tantance barazana na 2025 da ofishin daraktan hukumar leken asiri na kasar Amurka ya fitar. Inda ya ce, kasar Amurka ta kan zargi wasu da ayyukan da ita kanta ta aikata ko kuma take kan aikatawa, lamarin da ba wai kawai ya kasance babbar hanyar kai wa kasar Sin hare-hare ta yanar gizo ba, har ma ya kasance sananniyar barazanar intanet a duniya. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp