Batun bude iyakokin Nijeriya, na daga manyan batutuwan da za a ga sun mamaye kafafen yada labarai da na zumunta a yau cikin wannan Kasa. Wasu na murnar a bude, wasu na marasa baya game da budewar.
A fili ne yake cewa, sama da kashi 90% na al’umar Nijeriya, na da ra’ayin lallai ne a gaggauta bude wadancan iyakoki na dandagaryar kasa, wadanda a kansu ne ake magana sabanin iyakokin ruwa da ke a can kudancin Kasar. Dandazon mara-baya da aka samu daga ra’ayoyin akasarin jama’a, ya samu ne duba da irin mugun tashin gwauron zabi da daukacin kayaiyaki musamman na abinci da suka yi a daukacin sako da lungu na Kasar.
- Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Kudurin Dokar Bude Iyakokin Nijeriya Da Nijar
- Kisan Sojojin Kasar Nijar 29 Ya Ja Hankalin Shugabannin Afirka
Tun daga Shekarar 2018 ne gwamnatin tsohon shugaban Kasa Buhari ta ba da umarnin dode kan-iyakokin na kasa a Nijeriya, tare da gabatar da hujjar cewa, ta hanyar rufe wadannan iyakoki ne za a kaucewa duk wasu yunkuri na shigo da miyagun kayaiyaki da suka saba da doka zuwa cikin Kasar. Ke nan, irin wadancan kayaiyaki za su hadar da muggan makamai ne da wasu daidaiku ko gungun mutane za su yi yunkurin shigo da su cikin Kasa. Bugu da kari, hodar ibilis da sauran miyagun kwayoyi ma na daga sawun abubuwan da za a kaucewa shigo da su cikin Kasar, ta hanyar rufe wadancan kan-iyakoki.
Cikin Shekarar 2021 ne tsohuwar gwamnatin Buhari, ta fara yin mi’ara koma baya, tare da bude wasu daga irin wadancan iyakokin kasa da aka rufe tsawon Shekaru uku, inda ta yi kokarin bude wasu daga cikinsu. A Shakarar ne aka bude iyakar Seme da ke a yankin kudu maso yammacin Kasar. Ita ma iyakar Illela da ke a yankin arewa maso yammacin kasar, an bude ta ne a Shekarar ta 2021. Sai kuma iyakar Mfun da ke a bangaren kudu maso kudancin kasar, ita ma an bude ta ne tare da wadannan iyakoki biyu da aka ambata, Seme da Illela.
Bayan bude wadancan iyakoki da ke a sassa uku na wannan Kasa cikin Shekarar 2021, gwamnatin Buhari ta ci gaba da jaddada cewa, har yanzu akwai haramcin shigo da Shinkafa, Kaji, Agwagin-gis da wasu kayaiyaki da aka lasafta daga Kasashen Waje. Ke nan, an faiyacewa jama’ar Kasa fa’idar ci gaba da noma shinkafa, kiwon kaji da sauransu, don samun wadatarsu a cikin gida Nijeriya, tare ma da fara tunanin fitar da su zuwa ga Kasashen waje bayan sun wadace mu.
Wani abin takaicin shi ne, duk da waccan manufa da tsohuwar gwamnatin Buhari ta zo da, na garkame iyakokin Kasa, hakan bai hana samun ci gaba da yin fasa-kwabrin albarkatun man fetur na Kasa ba. A daya hannun kuma, maimakon kayan da ake sana’antawa a cikin Kasar su wadata, farashinsu yai kasa, gwargwadon samun talaka, sai akasin hakan ne ke ta faruwa. Lokacin Buharin, kayaiyaki a Kasar, sun yi mummunan tashi maimakon sauka, irin tashin da ba a yi tozali da shi ba, sama da Shekaru 30 da suka gabata a Kasar.
Sakamakon irin wannan mummunar canjin alkibla, sai aka wayigari tattalin arzikin Kasar kullum na kara taba kasa ne maimakon habaka.
Kungiyar ECOWAS Da Bude Iyakoki
A cikin Shekarar 2022, tawagar Kasashen da ke karkashin kungiyar ECOWAS ciki har da Nijeriya, sun yarda da bude daukacin kan-iyakokinsu ga juna. Ma’ana, duk wata Kasa cikin Afurka da ke cikin Kungiyar, za ta bude kan iyakarta ne ga “yar’uwarta “yar kungiya, ta yadda kai-tsaye dan wannan kasa zai shiga cikin waccan kasa, ba tare da samun wani shinge ko wata kuntatawa ba. Ta hanyar bude iyakokin ga juna, an gabatar da bukatar samun sukunin kasuwanci a tsakani. Ta yadda mazauna kasar Niger kan sami damar shigowa Nijeriya da kayaiyakinsu da ake da muradin saya a Nijeriyar. Shi ma dan Nijeriya, na da cikakkiyar damar shiga Niger, niki-niki da irin nasa kaya don cefanarwa, ko sayo kaya daga Niger din, tare da yin safararsu zuwa cikin Nijeriya.
Duk da irin wancan matsaya ta kungiyar ECOWAS, na a bude iyakokin daukacin Kasashen “ya”yanta, jagororin kamfen din kujerar shugaban Kasa ga Tinubu, a duk sa’adda suka zo yin wani gani da kungiyar masu noma ko sana’anta Shinkafa a Kasa, suna tabbatar musu ne da cewa, su fa, ba za su bude kan-iyakokin Kasa don shigo da shinkafar waje ba. Sukan ma ba su shawarar cewa, ka da su kuskura su zabarwa Kasa wani mutumin da idan ya sami nasarar zama shugaban Kasa a zaben Shekarar 2023, zai bude boda a shigo da shinkafa. Da irin wannan kamfen na fuska-biyu ne tawagar kamfen din Tinubu, ta sami nasarar kandamo dubban daruruwan kuri’u daga masu sabgar shinkafa a Nijeriya.
Atiku Abubakar, na daga “yan takarar kujerar shugabancin wannan Kasa da tun a lokacin kamfen ba su tasamma yin fuska sama da guda ba, game da lamarin bude boda koko dodeta?. Idan za a iya tunawa, sa’adda Atikun ya zo yin kamfen a jihar Kebbi, kai-tsaye ne ya labartawa jama’ar jihar cewa, a shirye ne yake na ya bude iyakokin wannan Kasa, muddin ya sami nasarar lashe zaben kujerar ta shugaban Nijeriya a zaben Shekarar 2023.
Wasu na da tunanin cewa, da siyasar Nijeriya ta balaga irin ta Kasashen Amurka da Ingila ko Faransa, babu makawa da yanzu shugaba Bola Tinubu ya fara samun zazzafar tirjiya daga manya manyan manoman shinkafa a wannan Kasa, duba da irin alkawarin da tawagar kamfen dinsa ta yi, na kin bude iyakokin wannan Kasa a shigo da shinkafar waje, muddin ya sami nasarar zama shugaban Kasa. Gashi ya kai ga nasarar, tare da balla musu wancan alkawari.
Wasu Na Maraba Da Bude Iyakokin
Kamar yadda aka fara bincinawa a farkon wannan rubutu cewa, akasarin al’umar Nijeriya musamman marasa karfin tattalin arziki, za a samu suna masu murna da san- barka ne game da yunkurin bude iyakoki da gwamnatin Ahmad Bola Tinubu ke yi a yau. Ba ya ga gama-garin mutane, ta tabbata ma wasu fitattun mutane, masana da manyan “yan siyasa, suma suna masu nuna goyon bayansu ne ga azamar bude bodoji da gwamnati ta tasamma yi.
Sanata Shehu Sani da ke jihar Kaduna, shi ma na daga mutanen da suke mara-baya ga wannan sabon kudiri na bude iyakokin Nijeriya karkashin umarnin shugaba Tinubu. Ga wasu daga dalilan da Sanata Sani ya gabatar, wadanda yake gani sun isa zama hujja karba6biya ga duk wanda ke da ra’ayi irin nasa;
i- Bude iyakokin, zai zamto yin biyaiya ne ga dokoki da kuma tanade-tanaden Kungiyar ECOWAS ne.
ii- Rufe iyakokin, ya gurgunta tattalin arzikin Nijeriya ne maimakon ya inganta shi.
iii- Dalilin rufe bodar, da dama daga “yan Nijeriya, sun sami kansu cikin mummunan talauci ne.
ib- Rufe iyakokin, ya gaza samar da yanayin da abinci zai wadata a Kasa.
b- Rufe bodojin, ya ba da makauniyar dama ga masu karfin tattalin arziki a Kasa, ta hanyar sahale musu kan-iyakokin bakin ruwa. Su shigo da kayaiyakin dubban miliyoyin kudade, su kara arziki bisa arziki, su kuwa talakawa su kara talaucewa.
Gaskiyar magana, da mutumin Nijeriya zai nazarci irin wadancan dalilai da Sanata Sani ya gabatar, babu shakka akwai kanshin gaskiya ciki, duba da irin kangin rayuwa da al’umar wannan Kasa ta sami kanta bayan gimtse iyakokin Kasar.
Dabbaka Ka’idojin Kungiyar ECOWAS
Tun da har Nijeriya ta amince da zama guda daga kasashen da ke yin biyaiya da kundin dokokin Kungiyar ta ECOWAS, to fa wajibinta ne ta dabbaka ka’idojinta. Bugu da kari, sai ma gashi karkashin mulkin na shugaba Tinubu, an wayigari shugaban Nijeriya ne shugaban kungiyar ta ECOWAS. Ke nan, Nijeriya ce ma mafi cancantar a ga tana dabbaka manufofin Kungiyar sama da sauran kasashen da suke mambobinta ne.
Durkushewar Tattalin Arzikin Nijeriya
Duk mai nazari ko bibiyar lamuran tattalin arzikin wannan Kasa, daga lokacin da Buhari ya zamto shugaban Kasa daga Shekarar 2015 har zuwa saukarsa, tattalin arzikin Kasar na yin baya ne akai akai. A kullum kididdigar Kasa da ta Bankin Duniya, na nuna koma bayan tattalin arzikin wannan Kasa ne dare da rana.
A kullum, kididdigar durkushewar kanana da matsakaitan masana’antu ne ke ta kan afkuwa. Ga rashin wadatacciyar wutar lantarki. Ga rashin samun cikakken sanya hannun gwamnati cikin sha’anin tada-komadar tattalin arzikin Kasa ga jama’ar Kasa.
Ba ya ga sha’anin kamfanoni da wutar lantarki, hatta ma harkar gona ba ta sami cikakken tallafin da ya kamace ta ba. Tallafin gwamnati, na wuyar kai wa ga hannun marasa galihu. Mu duba mu ga lamarin takin zamani, sai aka wayigari shi ma ya zama tamkar wani kayan gabas ne, ga tsada, ga rashin samun wadatuwarsa ga manoma matalauta. Irin wadannan lalatattun manufofi na tsohuwar gwamnati, sun taimaka ainun wajen durkushewar duk wani sako da lungu da zai taimaka zuwa ga bunkasar tattalin arzikin Kasa hada da na daidaikun mutane.
Irin wadancan dalilai na gaba kura baya sayaki, sun taka muhimmiyar rawa ainun, wajen kawo rashin aikin yi ga jama’ar Kasa. A karshen lamari, sai rufe bodojin ya zamto wani abu mai kama da wasan kwaikwayo, ganin duk wata hujja da tsohuwar gwamnati ta kafa don halasta gimtse iyakokin, ba su haifewa Kasa wani da mai ido ba.
A fili ne yake karara, tsirarin masu arziki, sun kara kudancewa ne matuka a lokacin Baba Buhari, a daya hannun kuwa, mafi akasarin talakawa sai kara ninkaya ne suke yi cikin tekun talauci dare da rana. Wannan ne babban dalilin karuwar miyagun aiyukan ta’addanci a Kasar.
Shi ma Farfesa Job Nmadu, na daga “yan Nijeriyar da suka yi na’am da sake wangale iyakokin wannan Kasa, bayan dode su da gwamnatin Buhari ta yi. Ga irin nasa dalilai da ya gabatar kamar haka;
i- Bude iyakokin, zai taimaka zuwa ga saukaka kai-kawon halastattun kaya, daga nan zuwa can.ii- Bude iyakokin, zai taimaka zuwa ga samarwa da gwamnati karin samun mamakon kudaden shiga.
iii- Tun da Kungiyar ECOWAS ta nema, lallai ne Nijeriya ta dabbaka.
ib- Bude bodojin, zai taimaka zuwa ga saukar farashin kayaiyaki tare da magance irin tashin da farashin kayaiyaki ke yi a yau.
Wasu manazartan na da tunanin cewa, tsohuwar gwamnatin Buhari, ko kadan ba ta yi dogon tunani da nazari ba, wajen gimtse wadannan iyakoki da ake kokarin sake budewa a yau, duba da irin yanayi na talauci da jama’ar da ke makotaka da iyakokin suka afka ciki. Dubban samari a garin Daura da kewaye, sun rasa aikin yi sakamakon dode iyakokin dandagaryar kasa a Nijeriya.
Gabanin rufe bodojin, suna amfani ne da dubban baburansu wajen yin fiton Shinkafa daga iyakar Nijeriya da Nijar. Sa’adda wadannan dubban samari suka rasa aikin-yi bayan rufe bodar Nijeriya da Nijar, an yi hasashen fadawar wasunsu cikin aiyukan ta’addanci ne!!!.
Hatta wadansu manoma da ke noma auduga da sauran dangoginsu, sun yi matukar murnar bude irin wadannan iyakoki.
Da yawan masu sabgar Shinkafa a Nijeriya bayan rufe bodojin, an zarge su ne da muzgunawa jama’ar Kasa, ta hanyar dandana musu mugun farashin shinkafar.
An hana shigo da shinkafa, sun gaza wadatar da Kasa da ita gabanin fara tunanin fita da ita zuwa ga Kasashen waje, uwa uba, samun ikon cin shinkafar, sai ya fara fin karfin akasarin jama’ar Kasa. Saboda haka, jama’a na jin za a bude bodojin, ban da murna da furta bakaken kalamai ga masu sabgar Shinkafar, babu wani abu da suke yi. Wasu na ganin, IDAN BERA NA DA SATA, TO ITA MA DADDAWA NA DA WARI!!!.