A kididdiga ta baya bayan nan daga hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta UNESCO ta bayyana cewa, Nijeriya na da yara fiye da Miliyan 20 da ke gararamba a titunan kasar ba tare da zarafin zuwa makaranta ba, wanann na nuna cewa, kashi 10 kenan na adadin al’umma kasar da aka kiyasta sun kai Miliyan 200 wanda bai kamata a yi watsi da shi ba.
A bayyane yake cewa, Nijeriya na da kyawawan dokoki da ke tabbatar da ba a bar wani yaro a baya ba a kan abin da ya shafi samar da ilimi, amma abin takaici shi ne a kullum yara na fuskantar gaggarumin cikas a kokarinsu na samun ilimi a sassan kasar nan, yawansu kuma na karuwa a duk shekara. A tsawon lokaci kididigar yawan yara da basu zuwa makaranta ya tsaya a tsakanin yara miliyan 10.5 zuwa miliyan 13.5 million sai a wannan lokacin ya yi tashin gwauran zabo.
Wannan rahoto na UNESCO ya zo wa al’umma da dama a matsayin abin mamaki, musamman ganin cewa, jihohi da dama a fadin tarayyar Nijeriya suna da tsari na bayar da ilimi kyauta kuma dole ga yara tun daga matakin Firamare har zuwa karamar sakandire wanda yara masu shekara 14 za su amfana. Babu wata wahalar fahimtar cewa, ko dai tsarin da aka yi na bogi ne ko kuma ba a tsayu don ganin an aiwatar da shi ba yadda yakamata.
Koma menene matsalar, tsarin dokar nan ta UBE ta shekarar 2004 ya ayyana bayar da ilimi kyauta kuma dole ga dukkan yara masu shekarun matakin Firamare da karamar sakandere a fadin tarayyar Nijeriya. Akwai kuma daftrarin dokar kare hakkin yara na ‘Child Rights Act’ wanda ya tabbatar da hakkin bayar da ilimi ga yara har zuwa matakin karamar sakandire ga dukkan yaran kasar nan.
In aka yi la’akari da wadannan ya zama dole mutum ya yi kokarin neman sainn dalilin da ya haifar da yawan yaran da basa zuwa makaranta musamman in aka lura da tasirin hakan ga tsaron yaran da kuma tsaron kasar gaba daya.
A ra’ayinmu, lalle wannan tashin hankali ne, in aka bar yara miliyan 20 suna gararamba a titunan Nijeriya ba tare da an san yadda za a koma da su makaranta ba don suna iya zama abubuwan da ‘yan ta’adda za su iya amfani da su wajen haifar da matsala tsaro a Nijeriya.
Akwai dalilai da dama da suka haddasa yawan yaran nan da basu zuwa makaranta. Daya daga cikin dalilan shi ne yadda aka yi watsi da makarantun gwamnati a dukkan matakai. Da yawa daga cikin makarantun sun lalace suna cikin yanayi mara kyau kuma gashi makarantu masu zaman kansu sun fi karfin talaka, ba za su iya biyan kudaden irin wannan makarantun ba.
Haka nan kuma a wasu lokutta, tafiya zuwa makarantun na iya zama da hadarin gaske ga wasu yaran. Iyaye da dama suna kin aika yaransu makaranta musamman yara mata don kare su daga cinzarafi da kuma musgunawa da suka shafi fyade da sauransu. Wasu yara da dama a yankunan karkara sai sun yi tafiya mai nisa kuma mai hadari kafin su isa makarantun su don daukar darasi.
Wasu yaran ma sai sun yi tafiya mai nisan gaske cikin tsaunuka, a nan yaran da ke fuskantar rayuwar talauci yana matukar sauki su yi watsi karatun in sun kasa samun mafita. Budu da kari matsalar tsaro da ta shafi garkuwa da ‘yan makaranta musamman a Arewancin Nijeriya, iyaye da dama suna daridarin kai ‘ya’yansu makaranta.
Abin takaci ne a ra’ayinmu da gwamnatin tarayya dana jihohi basu damu da karuwar yawan yaran da basa zuwa makaranta ba musammana arewacin Nijeriya musamman ganin suna sane da cewa, a kan tituna ake daukar nau’in bata gari da suke dawowa su kuma addabi al’umma.
Babu tantama babban jarin duk kasa shi ne yawan al’ummarta, kididdgar da muke da ita ta nuna cewa, muna da al’ummar da suka kai mutum miliyan 216, daga ciki kuma mun yi asarar yara miliyan 20 da basu samu alfarmar samun shiga makaranta ba.
A ra’ayinmu, babu yadda yaran da wannan abin ya shafa za su zama cikin wadanda za su tallafa wajen bunkasa kasa don basu samu damar bunkasa kansu ba ta yadda za su amfani kansu ballantana su amfani iyalan su da al’ummar su dama kasa baki daya.
Daga dukkan alamu Nijeriya ta kuskure a lokacin da duniya ke yekuwar bayar da Ilimi kyauta kuma dole, gwamnati bata dauki al’amarin da muhimmancin da ya kamata ba, amma a ra’ayinmu abin ba wai damar ta kucce ba ne.
Gwamnati na iya fara daura damarar tsamar da yara miliyan 20 din nan daga kan tituna suna zuwa makarantu. In har bamu tura su makaranta ba, to muna kokarin kyankyasar wani tashin hankalin da yafi karfi na Boko Haram ne a halin yanzu.
Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar gwamnatocin jihohi suna iya fito da wani tsarin da za a mayar da irin wannan yaran zuwa makaranta na akalla shekara 6, wannan zai matukar taimakawa wajen kawar da yaran daga titunanmu hakan kuma zai bunkasa harkar ilimi a kasar nan.
Muna sane da cewa, shi al’amarin ilimi ba wai na gwamnati kawai ba ne kadai, dole bangaren kamfanonin masu zaman kansu su shigo tare da kuma iyaye, malaman addini, da shugabanni na da rawar da ta yakamata su taka. Gaba daya in muka hada hannun zamu tabbatar da kawar da wannan matsalar kafin ta zama gagarabadau.