Jim kadan bayan wata takaitacciyar ziyara a hadaddiyar daular Larabawa, UAE, shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya isa Kasar Saudiyya don wata tattaunawa ta musamman da Yarima Muhammad bin Salman.
In ba a manta ba, kasar Rasha ta fitar da wata sanarwa da ke nuna cewa, Shugaba Putin zai amshi bakuncin shugaban kasar Iran, Ibrahim Ra’isi a Moscow, ranar Alhamis.
Tun bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC ta bayar da sammacin kama shi, shugaba Putin ya kai ziyara ne a ƙasashen da ba su amince da dokokin kotun ba kadai.