Aikin hako man fetur da gwamnatin tarayya ta kaddamar wata 16 da suka wuce a garin Kolmani da ke Jihar Bauchi ya tsaya cik, mazauna garin sun bayyana cewa, tuni suka ga ana kwashe kayyakin aikin zuiwa wasu wuraren daban.
A watan Nuwamba, shekarar 2022 ne a kusan karshen mulkin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Kamfanin NNPCL ya fara shirin hako danyen man fetur a rijiyoyi 2 da ke garin Kolmani wanda ke a tsakanin jihohin Bauchi da Gombe, an sanya wa rijoyin sunan OPL809 da OPL810.
- Rundunar ‘Yansandan Bauchi Ta Fara Cafko Masu Garkuwa Ta Amfani Da Fasahar Zamani
- Mun Gano Famfo 5,570 Da Ake Amfani Da Su Wajen Satar Danyen Mai — NNPCL
Haka kuma an kiyasta cewa, man da ke shimfide a rijiyoyin ya kai fiye da ganga biliyan 1 ana kuma sa ran za a iya ci gaba da hakar man har zuwa shekarar 2060.
Masana sun kuma kiyasta za a iya samun nasarar hakar gangan danyen mai 50,000 a kullum in aka fara aiki gadangadan.
Amma kuma wani mazaunin yankin da ya bukaci mu sakaya sunansa ya bayyana cewa, an dakatar da aikin hakar man ne jim kadan bayan da shugaban kasa ya kaddamar da aikin, babu wani abin a zo a gani da aka yi wurin.
“A shekarar da ta gabata mun ga yadda jami’an hukumar NNPCL suka kwashe manyan kayayyakin aikin hako man zuwa Jihar Nasarawa an kuma wuce da wasu kayan zuwa tafkin tekun Chadi, a halin yanzu kusan babu wasu kayan aiki masu muhimmanci a Kolmani” in ji shi.
Bayanai sun nuna cewa, daga cikin rijiyoyi 5 da ake da su a Kolmani, 2 kawai aka fara aiki a cikin su tunda farko. Haka kuma gadar da ta hada garin na Kolmani da sauran yankuna ta rushe sakamakon manyan motoci da ke zirga-zirga a tsakanin yankin tunda aka fara hadahadar batun hako man fetur din.
Mazaunin garin ya kuma kara da cewa, “A ‘yan kwanaki kuma mun ga jami’an kanmfanin Sterling Global na kokarin gyara gadar, maganar nan da muke yi na ga manyan kayan aikin gyaran gadar sun fara zirga-zirga,”.
Game da batun samar da tsaro kuma, an gano cewa, fara aikin hakar man Kolmani ya taimaka wajen karfafa harkar tsaro inda a halin yanzu jami’an NSCDC da sojoji ne suke aikin samar da tsaro a yankin.
A halin yazu kuma duk kokarin jin ta bakin jami’an hukumar NNPCL da na ma’aikatar albarkatun man fetur a kan bayanin watsi da aka yi da hakar man Kolmani ya ci tira don babu wanda ya ce uffan a kan lamarin.
Mun Samar Da Yanayin Da Aiki Zai Tafi Lafiya kalau – Gwamnatin Bauchi
Kamishinan albarkatun kasa na Jihar Bauchi, Bello Maiwada ya bayyana cewa, gwamnatin Bauchi na tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki don ganin an ci gaba da aikin hakar man fetur a Kolmani.
“Lamarin hakar man fetur abu ne da ke karkashin alhakin gwamnatin tarayya a kan haka ba mu da wani abin cewa mai yawa a kai.“Amma a matsayin mu na jiha, mu na cikin masu ruwa da tsaki, saboda a kasar mu ake aikin, a kan haka dukkan matakin da za mu dauka zai zama daga wannan bangaren ne,” in ji shi.
Kwamishinan ya lura da cewa, lallai babu wani ci gaba mai muhimmanci da aka samu a harkar hakar mai a garin Kolmani tun bayan da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci kaddamar, sai dai Jihar Bauchi ta samar da dukkan abin da ake bukata na ganin hakar man ya samu nasarar da ke bukata.
“Mun samar wa kamfanin da ke aikin hakar man cikakken tsaro ga ma’aikatanta da kayan aikinta, ta yadda za su yi zirgazirga ba tare da wani tsoron wani abu zai samu rayuwarsu ba ko kuma kayan aikiinsu.
“Haka kuma gwamnatin Jihar Bauchi ta bude makarantar koyar da harkokin man fetur da gas, wanda shi ne na farko a jihohin arewa, mun yi haka ne don mu samar da kwararrun ma’aikatan da za su iya aiki a bangaren harkar hakar man feur din.
“Maganar da muke yin a yanzu an dauki dalibai 300 a harabar makarantar da ke Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Abubakar Tatari Ali Bauchi muna sa ran ci gaba da sauran kwasa-kwasai nan ba da dadewa ba.
Ana Ci Gaba Da Hakar Mai A Ebenyi Ta Jihar NasarawaBinciken LEADERSHIP ya nuna cewa kamfanin NNPCL na ci gaba da hakar man fetur a ‘Ebenyi-A well’ da ke a karanmar hukumar Obi ta jihar Nasarawa.
Wakilinmu ya gani cewa, wannan na faruwa ne duk da matsalolin da aka fuskanta na abin da ya shafi yanayin kasar.
A watan Maris na shekarar 2023 ne tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da hakar main a Ebenyi A oil well, wanda hakan ya nuna fara aikin hakar mai a yankin tsakiya Nijeriya.
Wannan yana zuwa ne bayan ziyaara da shugaban kamfanin mai na NNPCL, Mr Mele Kyari, ya nsanar yiyuwar samun danyen man fetur mai tarin yawa a yankin Keana da ke karamar hukumar Obi, bayan an yi shekaru ana fafutukar neman albarkatun man a yankin.
Mr Kyari ya kuma kara da cewa, kamfanin ya fara binciken enman man fetur din ne tun a shekarar 2010 amma aka dan samu cikas, saio gashi an samu nasarar a halin yanzu.Wani matashi a yankin mai suna Mr. Emmanuel Ogosi, ya bayyana wa walilanmu cewa, fara aikin hakar man ya sa su a farin ciki da musamman ganin lamarin zai bunkasa tattalin arzikinsu.
Ya kara da cewa, a halih yanzu ma wasu matasa suna nan sun fara kananan ayyuka a yankin da ake hakar man, harkokin kasuwanci ma ya fara kankama.