Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shaida wa ‘yan Nijeriya cewa bayan wuya, sai dadi, wannan matsin tattalin arzikin zai zo karshe nan ba da jimawa ba.
Ya ce abubuwa za su kyautata kar ‘yan Nijeriya su yi kasa a gwiwa.
- Matakin Kona Kai Da Sojin Amurka Ya Dauka Ya Diga Ayar Tambaya Ga ‘Yan Siyasar Amurka
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Samar Da Cibiyoyin Koyon Sana’o’i Fiye Da 24
Haka kuma shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ya bukaci ‘yan Nijeriya su kara hakuri tare da bayar da hadin kai ga gwamnati, domin ta kaddamar da wasu sauye-sauye kan tattalin arziki da za su rage wannan radadin.
Shugaban Tinubu da shugaban majalisa sun bayyana hakan ne a daidai lokacin da kungiyar kwadago ke gudanbar da zanga-zangar kan tsadar rayuwa da ya gudana a jihohi da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja a wannan makon.
Shugaban kasa ya ce, “Muna tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa bayan wuya, san dadi.
“A yanzu ana cikin mawuyacin hali, amma muna iya bakin kokarinmu wajen magance lamarin.”
Shugaban majalisar wakilai ya bayyana cewa akwai abubuwa da dama da gwamnati take kokarin saidawa ta yadda za su amfanan da ‘yan Nijeriya. Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su kara hakuri, saboda dade bai samuwa sai an sha wuya.
Ya ce, “Na san da cewa akwai tallafi masu yawa da karin albashi da kuma sauye-sauye da za su kawo walwala suna nan tafe nan gaba kadan.
“Mun san irin wahalar da ake sha a halin yanzu, za mu yi iya bakin kokarinmu wajen kawo saukin rayuwa a Nijeriya. Muna bukatar a ba mu lokaci.”