Dangane da jawabin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi a baya-bayan nan game da kasar Sin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau a kullum Talatar nan cewa, Amurka ce kasar da ta fi yawan samar da makamai a yakin da Ukraine ke yi. Tuni bayanai suka fallasa ikirarin Amurka na kare zaman lafiya tare da fallasa hakikanin fuskarta game da “tsoron cewa, duniya ba za ta kasance cikin hargitsi ba”.
Ya bayyana cewa, kasar Sin ita ce mai kare tsarin kasa da kasa, kuma a ko da yaushe tana kiyaye tsarin kasa da kasa tare da MDD a matsayin jagora da tsarin kasa da kasa bisa dokokin kasa da kasa. (Mai fassarawa: Ibrahim)