Aikin Hajji yana da nau’o’i guda uku, akwai Kirani, Tamattu’i da kuma Ifradi. A nau’in Hajjin Kirani, idan mutum zai yi niyya, zai hada Umura da Aikin Hajji a ciki lokaci daya ba tare da rarrabewa ba. Ma’ana ya ce “Na yi niyyar Hajji da Umura”. To idan ya yi Dawafi da Safa da Marwa, sun zama na Hajji da Umura tunda dama a hade ya yi niyya. Haka nan bayan an sauko Arfa ya yi Jifan ranar Sallah, zai sake zuwa ya yi Dawafin sauka Arfa, sannan ya yi Safa da Marwa idan ya kasance bai yi na farkon zuwan sa ba. Idan ya yi na a farkon bayan kammala Dawafin shiga Makka, shikenan wannan ya isar ma sa.
Hajjin Tamattu’i kuwa, mutum zai yi niyyar Umura ce ita kadai idan ya zo mikati. Ba zai hada niyyarta da ta Hajji ba. Idan Alhaji ya yi umurar ya gama ya yi aski, to ba zai kara yin komai ba sai dai ya jira zuwa ranar takwas ga wata ko ranar da za fita zuwa Minna ya yi niyyar Aikin Hajji daga masaukinsa. Domin hukuncinsa iri daya ne da na Dan Makka a lokacin. Ba sai ya je wani wuri ba da nufin yin harama. Umura ce idan ‘yan Makka ko bakin da ke zaune a nan za su yi, sai sun fita zuwa Tan’im su yi harama, kamar yadda shari’a ta tanadar.
Shi kuwa Alhajin da zai yi nau’in Hajjin Ifradi, tun daga mikati zai yi niyyar Hajji. Kuma idan ya kammala Dawafin shiga Makka da Safa da Marwa (idan ya yi), ba zai warware haramarsa ba har sai bayan ya kammala Aikin Hajji saboda ya koro abin hadayarsa.
Dama sharadinsa (Ifradi), Alhaji ya kasance ya taho tare da abin hadayarsa. Idan ya yi Safa da Marwa a farkon zuwan sa, shikenan ba sai ya kara yi ba wannan ya isar ma sa. Idan bai yi ba, sai ya yi.
Abin lura a nan shi ne, duk wanda ya yi niyya da Hajjin Ifradi ko Kirani, idan ya yi Safa da Marwa bayan ya yi Dawafin shiga Makka (Dawaful Kudum), to ya isar ma sa ba sai ya sake yi bayan Dawafin sauka daga Arfa (Dawaful Ifadah) ba. Amma shi mai Hajjin Tamattu’i zai sake yi, ma’ana bayan Safa da Marwan da ya yi na Umura, zai kara yi bayan ya yi Dawafin sauka daga Arfa. Ma’ana shi sau biyu zai yi Safa da Marwa.
Da Alhajin da ya yi Tamattu’i da wanda ya yi Kirani duk za su ba da hadaya daidaita gwargwadon iyawarsu daga kan Akuya ko Rago ko Saniya ko Rakumi.
Amma an fi so a yi da Rakumi ga wanda yake da iko. A Aikin Hajji, an fi son yawan nama sabanin Layya da aka fi son nama maidadi da kitse. Shari’a ta yarda mutum bakwai su hada kudi su sayi Rakumin hadaya guda daya.
Idan Alhajin da hadaya ta hau kansa bai samu dabbar da zai yi ba, sai ya yi azumi na kwana uku a Makka kafin a fita zuwa Arfa idan zai yiwu. Idan bai samu dama ba sai ya yi bayan Arfa kafin ya bar Makka. Bayan ya dawo garinsu, sai ya yi sauran azumin kwana bakwai. Jimillar azumin kwana 10 ne yake madadin hadayar da bai yi ba.
Amma kuma kar ya zama Alhaji yana da halin yin hadayar sai ya yi wa Allah rowa ya ki yi ya ce shi azumi zai yi. Wannan babu kyau.
Ana samun wadanda suke da halin kudi su ki yi, sun gwammace su kullo kudin guzurinsu su dawo da shi gida, wannan yi wa Allah rowa ne.
Azumin da aka ce a yi na kwana uku a Makka da kwana bakwai a gida, ya ta’allaka ne ga wadanda ba su da halin yin hadaya kwata-kwata. Ko ya kasance idan suka sayi dabbar hadayar za su galabaita saboda karancin kudin abincinsu.
Don Allah jama’a mu kiyaye. Rowa haka kawai ma babu kyau a addini ballantana kuma wurin yin ibada.
Malamai Fakihai, Allah ya yarda da su, sun yi sabani a kan a cikin nau’o’in Aikin Hajjin nan uku; wanne ne ya fi.
Shafi’awa sun tafi a kan cewa Ifaradi da Tamattu’i sun fi Kirani a wurinsu. Domin a fahimtarsu, Kirani kamar Tamattu’i ne kawai. Har ila yau, a cikin su Shafi’awan akwai wadanda suke ganin yin Tamattu’i ya fi, akwai kuma wadanda suke ganin yin Hajjin Ifradi ya fi sauran.
A wurin Malikawa, Ifradi ya fi sauran. Hanabilawa kuwa sun tafi a kan cewa yin Hajjin Tamattu’i ya fi Kirani kuma ya fi Ifradi. Saboda Tamattu’i ya fi sauki ga mutane, domin musamman mutanen da suke kasashen da ke nesa da Makka, ba za su iya kore dabbobin hadayarsu zuwa can ba (musamman a wannan zamanin). Kuma sun ce Tamattu’i ne Annabi (SAW) ya yi burin yi, ba domin ya taho da dabbobin hadayarsa ba.
Imam Muslim ya ruwaito Hadisi daga Ada’u ya ce “Na ji Jabir bin Abdullahi (RA) ya ce ranar da muka zo Aikin Hajji (lokacin farko da Annabi (SAW) ya ce a zo a ga yadda zai yi), mu Sahabbansa dukkanmu mun yi niyyar Aikin Hajji ne kadai – ba tare da Umura ba.
Sai Annabi (SAW) ya zo mana kashe-gari ya umurce mu mu warware haramarmu, mu sadu da iyalanmu. A wannan lokaci ba wai tilasta mana ya yi a kan haka (saduwa da iyali) ba. Amma ya halasta saduwa da su ne don nuna warware harama. Sai muka ce ma sa – Ya Rasulallah (SAW) – tsakaninmu da ranar Arfa bai fi kwana biyar ba. Yanzu za mu iya zuwa Arfa alhali mun sadu da iyali? Sai Annabi (SAW) ya mike a cikinmu ya ce, “Jama’a ku sani fa na fi ku tsoron Allah, na fi ku gaskiya fa, ni kaina ba don wannan hadayar tawa ba; ni ma da na warware kamar yadda za ku warware. Idan na sa gaba kan abin da Allah ya ce in yi ba na juya baya, don haka ku warware.” Sai muka ce mun ji mun bi.”
Daga ma’anar wannan Hadisin, Hanabilawa sun fi kusa kenan da abin da Annabi (SAW) ya so wa al’ummarsa a cikin wadannan nau’o’in Hajjin guda uku.
Ya halasta idan wani Alhaji duk bai san wadannan nau’o’in Hajjin ba, a gwaggwada ma sa yadda zai yi Aikin Hajjin (ko da bai ambaci nau’in da zai yi ba), bayan an gama sai a yi ma sa aski ya warware haramarsa kuma Hajjinsa ya yi.
•Abubuwan Da Aka Halasta Wa Mahajjaci
Daga lokacin da mutum ya yi harama da aikin Hajji, duk wani abu na kayan ado ya haramta gare shi, sai dai abin da ba a rasa ba.
Daga cikin abubuwan da aka halasta ma sa akwai yin wanka idan ya yi dauda, watakila saboda doguwar tafiya ko kuma wanda yake Hajjin Ifradi ne da zai kwashe wasu kwanaki cikin harama ko ga wanda ya samu janaba.
A cikin Muwadda, Imam Malik ya ruwaito daga Nafi’u, daga Abdullahi bin Umar (RA) cewa shi (Abdullahi bin Umar) ya kasance yana yin wanka kuma har ya wanke kansa alhali yana cikin harama. Abin da ya sa ake tsoron wanke kai shi ne don a kiyaye cire gashi.
Har ila yau, a cikin Muwaddan, Imam Malik ya ce Abdullahi bin Umar ba ya wanke kansa idan ya zo yin wanka bayan ya yi harama har sai idan ya samu janaba.
Imam Malik ya karhanta mutumin da ya yi harama ya game kansa da ruwa (kurmani).
Malamai sun ce ya halasta a yi wanka da sabulu bayan an yi harama domin cire dauda. Kuma ya halasta a goge baki da makilin da sauran su. Wannan ma ya halasta a wurin Hanabilawa da Shafi’awa ba ga Malikawa ba kawai, koda kuwa sabulun yana da kamshi.
Ya halasta mai harama ya rufe fuskarsa saboda warin wani abu ko kura.
Idan mai harama ya rufe kansa da mantuwa ko saboda rashin sani, babu komai a kansa. Sai dai kawai a ce ma sa ya cire. Haka nan wanda ya yanke farcensa da mantuwa ko rashin sani, sai ya yi Istigfari.
Ya halasta ga mai harama ya yi kaho idan ya kamu da rashin lafiya. Zai iya matse kurji ko cire hakori ko yanke wata jijiya a jiki ko wani abu da za a yi wa mai harama a asibiti don ya samu lafiya. Ya tabbata cewa an yi wa Manzon Allah (SAW) kaho a tsakiyar kai alhali ya yi harama da Hajji.
Imamun Nawawi ya ce sun tafi a kan cewa za a iya yi wa mai harama kaho koda kuwa za a yanke gashi a wurin. Yin hakan babu laifi, amma kawai haka mutum ya sa a yi ma sa ba tare da wata bukata ba, wannan laifi ne.
Ya halasta ga mai harama ya yi susa a jikinsa. An tambayi Ummul Mumina Aisha (RA) cewa mai harama zai iya yin susa? Ta ce “eh, zai ma iya kai isa matuka wurin susan jikinsa”.
Babu laifi ga mai harama ya shaki kamshi ko ya kalli madubi. Sai dai Malikawa da Hanafiwa sun karhanta zama a wurin da yake akwai turare mai kamshi.
Haka nan, babu laifi mai harama ya daura jakar kudinsa a jikinsa ko sanya zobe a hannu. An ruwaito wannan daga Abdullahi bin Abbas (RA).
Ya halasta mai harama ya sanya kwalli na magani (idan idonsa yana ciwo), matukar kwallin ba mai hade da turare ba ne.
Babu laifi mai harama ya yi amfani da lema saboda ruwa ko rana ko kuma ya shiga cikin wata rumfa.
Mace za ta iya yin kunshi (lalle) kafin ta yi harama da Hajji, amma ban da bayan yin harama. Domin Malaman Malikawa da Hanafiyawa sun ce yin lalle bai halasta ba a ko wane bangare na jiki bayan an yi harama, walau a wurin mace ko namiji.
Wakazalika, babu laifi mai harama da Hajji ya kashe dabbobi masu cutarwa. Annabi (SAW) ya lissafa wasu dabbobi a matsayin fasikai da za a iya kashewa wadanda suka hada da: Hankaka, Shirwa, Kunama, Bera da Kare Mai Cizo.
Haka nan za a iya kashe maciji, zaki, damisa, kura da sauran abubuwa masu cutarwa. Masu dabbobi za su iya kashe kaska. Shi ma dan fashi za a iya yakarsa.
A takaice dai duk wani abu mai cutarwa za a iya kashe shi, amma idan ba ya cutarwa ko an gan shi kar a taba shi.
A mako mai zuwa, za mu zo da abubuwan da aka haramta wa mai harama da aikin Hajji ya yi, in sha Allahu.