Ta tabbata ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich ta lashe gasar Bundesliga ta bana bayan da Bayer Leverkusen ta buga canjaras a wasanta da Freiburg yau Lahadi.
Itama Munich canjaras ta buga a wasanta na ranar Asabar tsakaninta da RB Leipzig inda aka tashi da ci 3-3, amma kuma sakamakon wasan Bayer Leverkusen dake matsayi na biyu ya tabbatarwa Munich nasarar lashe gasar Bundesliga karo na 34 a tarihinta.
- Harry Maguire Ya Sanya Hannun Kwantaragin Shekara Ɗaya A Manchester United
- Dortmund Ta Doke Bayern Munich A Wasan Hammayya A Gasar Bundesliga
Za a iya cewa kocin ƙungiyar Vincent Kompany, wanda ya karɓi aikin horar da ƙungiyar bayan korar Thomas Tuchel ya shigo da kafar dama, wannan ne karon farko da tsohon Kocin na Burnley zai lashe wata gasa tun bauan fara aikin koci.
Za a baiwa Bayern Munich kofin a wasanta na gaba da zata buga da kungiyar kwallon kafa ta Borrusia Monchengladbach a filin wasa na Allianz Arena dake birnin Munich, inda akwai yiwuwar wannan ce kakar wasa ta karshe ga mataimakin kyaftin din ƙungiyar Thomas Muller.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp