Mahukunta a birnin Beijing sun shirya fadada yankin koli, na gwajin motocin hawa masu tuka kan su zuwa kimanin sakwaya kilomita 3,000, tsakanin babban shatale-tale na 4 da na 6 dake birnin, fadin wurin da zai haura ninkin gundumomin birnin 6.
Da yake tabbatar da hakan a ranar Juma’a, yayin taron karawa juna sani na kasa da kasa na shekarar 2024, don gane da hade sassan tsarin aikin ababen hawa masu sarrafa kan su, darakta a ofishin lura da yankin gwajin motocin masu tuka kan su na birnin Beijing Wang Lei, ya ce tun bayan kaddamar da yankin farko na gwajin a kasar Sin, a watan Satumba na shekarar 2020, birnin ya cimma nasarar samar da tsarin kayayyakin gudanarwa masu aiki da na’urori masu kwakwalwa, a sassan yankin da ya kai sakwaya kilomita 600.
A cewar jami’in, fadada yankin gwajin na birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, wani kokari ne na sanya birnin zama a kan gaba, a fannin cin gajiyar fasahohin motoci masu tuka kan su. (Mai fassara: Saminu Alhassan)