Jami’an da ke gudanar da harkokin mulkin jama’ar birnin Beijing sun bayyana a gun taron manema labarai a ranar Talata cewa, za a gudanar da dandalin tattaunawa kan gaggauta mayar da martani ga korafe-korafen jama’a na birnin Beijing, daga ranar 18 zuwa ta 19 ga watan Disamba.
Manufar taron ita ce samar da dandalin kasa da kasa, inda kwararru za su yi musayar ra’ayi, da tattauna sabbin hanyoyin warware kalubale a fannin hidimar jama’a, da musayar gogewa a fannin gudanar da harkokin mulkin birane.
- Sarki Sanusi II Zai Sake Ayyana Wata Rana Ta Naɗa Sabon Hakimin Bichi
- Kotu Za Ta Saurari Ƙalubalantar Ikonta Da Emefiele Ke Yi Kan Shari’arsa
Darektan ofishin kula da harkokin gudanarwa da bayanai, Shen Binhua, ya bayyana irin kalubalen da ake fuskanta wajen gudanar da harkokin mulki a birnin Beijing. Yana mai cewa, don magance batutuwan da suka shafi manyan biranen, birnin Beijing, wanda ke da mazauna sama da miliyan 20, fiye da ninki biyu na yawan jama’ar birnin New York, ya gabatar da wani sabon shirin “gaggauta mayar da martani ga korafe-korafen jama’a” a shekarar 2019. Wanda ke da nufin mayar da martani cikin gaggawa ga bukatun mazauna da kuma magance matsalolin rayuwar yau da kullun yadda ya kamata.
Bayanai na hukuma sun nuna cewa tun lokacin da aka fara shirin, an saurari tare da warware kararraki sama da miliyan 150, tare da samar da mafita da gamsuwa na kashi 96.5 cikin dari da kashi 96.9 bisa dari, bi da bi. Wannan shirin ya hada hidimomin layukan waya sama da sittin zuwa hadaddiyar layin lambar wayar daya wato 12345. Layin yana aiki a kowace rana ba dare ba rana, tare da masu aiki sama da 1,700 suna karbar aiki bi da bi don amsa kira da aiwatar da bukatu, suna warware matsalolin kusan kowane bangare na rayuwar birni, gami da bayar da hidima na kasuwanci, da na kulawa da tsofaffi da yara, da kiwon lafiya, da ilimi da sufuri. (Mohammed Yahaya)