• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu

by Leadership Hausa
3 hours ago
Benjamin

Alokacin da wasu ke ta maganganun da basu dace ba domin nuna manufarsu, shi ya zaɓi tattaunawa da kuma kawo gyara.

Ɗan majalisa mai manufa maikyau

A matsayinsa na mataimakin Shugaban Majalisa Wakilai ta tarayya ta 10, Honorabul. Benjamin Okezie Kalu, PhD, CFR, ya samar da wani sabon babi na yadda ake tafiyar da jagorancin ita majalisar.

Domin kuwa ya haɗa rayuwarsa ta mai ilimi da sanin tafarkin diflomasiyya — yadda ake tafiyar da majalisar ba domin a samu kanun labaran da zasu ja hanklai ba, amma sai domin a yi wani tafarkin da zai samar da ci gaba.

  • Majalisa Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Kai Agajin Gaggawa Ga Waɗanda Fashewar Tanka Ta Shafa A Neja
  • Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe

Daga taron kawo gyara kan tsarin mulki zuwa ci gaban shiyya, tafiyar da al’amuran kafaɗa- kafaɗa da mata domin samun zaman lafiya, Kalu ya tsaya kai da fata wajen nuna abinda Shugabanci yake nufi lokacin da masu ilimi ko mai ilimi ya haɗu da wata manufa maikyau.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

Yana magana ko jawabi cikin hankali, amma kuma shawarwarin da yake badawa suna da matuƙar amfani wajen kawo gyaran wurare da dama.

Mai ilimi, tsara yadda za’a ɓullo ma al’amura, mutunci ga kuma kwarjini da ƙwarewa

An haife Kalu 5 ga Mayu, 1971, a Agbamuzu, a ƙaramar hukumar Bende ta Jihar Abia State, tarihin rayuwar Kalu ya fara ne daga aiki da kuma samun tallafin ƙaro ilimi.

Yana da digirin digirgir PhD a tsarin al’umma da kuma karatun abinda da wayo ake koyonsa (Jami’ar Abuja), da kuma LL.M akan ta’addanci da taimakawa kan jin ƙai  (Distinction, daga Jami’ar Kalaba), da MBA daga Jami’ar Oɗford Brookes  (UK), da kuma LL.B (Hons.) daga Kalaba.

Ya cigaba da karatu— halin yanzu yana karanta LL.D  a shari’a — hakan ya nuna  a gare shi cewa koyar yadda ake Shugabanci, wani babban lamari ne mai kamar ‘yan tagwaye .

Abinya zarce digirori, domin akwai ma ƙarin ilimin daya samu a makarantar Harɓard Kennedy , Jami’ar Miami, UNICRI (Italy), Jami’ar John Cabot ,  da kuma Chartered Institute of Arbitrators (UK).

Kowace takardar shedar karatun da ya yi ta ƙara faɗaɗa ma shi bunƙasar abinda yake son yi kuma gwanin ban sha’awa — duk wata wahalar wani lamari akan samu damar gano bakin zaren cikin sauri wajen samun dokar da ake buƙatar cimmawa.

Daga ƙaramar hukuma zuwa lamarin da ya shafi ƙasa

Kalu ya fara rayuwar siyasa ne tun a gida inda ya zama Shugaban ƙaramar hukumar Bende— damar da ya fara samu ya kuma yi amfani da ita wajen sa mutane cikin mulkinsa, lamarin da tun lokacin aka fara fahi,tar kowanen shi, amma abin shi ne har zuwa halin da ake cikin  yanzu.

Daganan ya riƙe muƙamin mai ba gwamnan Jihar Abia shawara kan muradan ci gaba da kuma hulɗa da ƙasashen waje, ta yadda ake maida ci gaban Karkara a cikin lamarin daya shafi ƙasashen duniya.

Lokacin da yazo Majalisar Wakilai ta tarayya a shekarar 2019, bai zo wurin ba da wata sha’awar ya zama wani abu ba, amma yana da wani ƙuduri na: ƙara faɗaɗa hukumomi, riƙa tafiyar da gwamnati da tausayin al’umma, yadda ake tafiyar da majalisar a mayar da lamarin shi ma na zamani.

A matsayin san a Shugaban kwamitin lamurran ‘yan jarida da kuma hulɗa da mutane na Majalisa ta 9, sai ya kasance wata murya ce ta Mjalisar — inda yake kare lamarin daya shafi tafiyar da al’mura da gaskiya, yayin da kuma faɗaɗa yadda mutane suka gane ayyukan ‘yan majalisa’.

Lokacin da aka shiga Majalisa ta 10, sai ‘yanuwansa ‘yan majalisar suka ɗaga likkafarsa zuwa mataimakin Shugaban Majalisar, ta haka ne kuma ya ƙara gogewa wajen ƙara fahimtar ayyukan Majalisar a matsayinsa na mataimakin Shugaban.

Abubuwan da ya yi a majalisa

‘Yan majalisa ƙaɗan ne a Nijeriya waɗanda suka a tarihin Nijeriyar yanzu da ake ciki za su iya fuskantarsa dangane da ayyukan Majalisar.

Kalu ya ƙaddamar da fiye da ƙudurori 120 — wani ci gaba ne da aka samu wanda ya shafe kusan gaba ɗaya na kowane ɓangare na gwamnati.

Ƙudurorin da ya gabatar sun haɗa da lamarin daya shafi gyaran tsarin mulki zuwa  gyara kan lamarin daya shafi shari’a, ƙoƙarin samar da daidaito tsakanin  jinsi,  ilimi, tattalin arziki, tsaro, da kuma yadda za a  kawo gyara kan lamarin daya shafi aiki.

Daga cikinsu akwai waɗansu da shawara ce aka bada kamar haka:

Hukumar kula da ci gaban yankin sashen Kudu maso gabas (SEDC) ƙudurin da aka shirya domin a sake gina sashen da ya haɗu da matsala lokacin da aka yi yƙain basasa na Nijeriya, abubuywan more rayuwa da kuma tattalin arzikin yankin.

Ƙudurin ‘yansandan Jiha, wata dama ce ta samar da jami’an tsaro waɗanda suka yi daidai da yadda irin tsarin gida yake na maganar tsaro.

Ƙuduri na mata waɗanda suke a majalisa saboda a samu yin gyara yadda mata ba ayi masu adalci a majalisa, a ware wasu kujeru musamman saboda mata.

Ƙudurin kafa Jami’ar kimiyyar lafiya ta gwamnatin tarayya a, Bende, da kuma kafa Kwalejin ilimi, duk, a Bende, kawo manyan makarantu a gida kuma mazaɓarsa.

Waɗannan ƙudurorin ko shawarwari ba wai sun kasance ‘yar shawara ce ba. Suna dai ɗauke ne da wata manufa na kawo gyara da kuma haƙurin da zai bada sakamako maikyau — manufa ce mai nuna abinda ake hasashe ko hgani a zuciya da irin fasaha ta majalisa su kan tafi tare.

Jagorancin da ya zarce majalisa

A matsayinsa na Shugaban kwamiytin gyaran tsarin mulki na 1999 , Kalu ya jagoranci ɗayya daga cikin aikin ƙasa mai muhimmanci da kuma wuya.

Abinda ake son ya yi shi ne: ya maida tsarin mulki na zamani, samar da wasu gyare- gyaren da z su taimaka nusamman ma wajenhaɗin kan ƙasa.

A aikin da ya yi nashi matsayin, ya taka rawa ta yadda zai kasance mai saurare ga waɗanda suke da ruwa da tsaki,  a samu yin daidaito wajen maganganun da suka shafi shiyyoyi, da tabbatar da kowa na bashi hakinsa na maganganun da ake ganatarwa lokacin gyaran.

Hakanan ma ya wakilci Nijeriya a taron ‘yan majalisu na duniya:

Shugaba, Kwamitin Majalisar ECOWAS kan lamarin daya shafi mulki, kuɗi da kuma kasafinsu

Mamba A Majalisar Afirka

Mamba na  kwamitin da zai zaɓi abinda da za’a tattauna na majalisar  ƙungiyar Kasuwanci ta duniya

Mamba na, majalisun ƙasa da ƙasa (IPU)

Dukkan waɗannan wuraren suna nuna ko wanene shi dangane da harkar majalisa saboda kuwa ai yana da ƙwarewa dangane da aikin majalisa da kuma muryar Afirka kan matakin da za’a ɗauka na duniya.

Kalu a ɓangaren mai zaman kansa

Nasarar da Kalu ya smu hakan ta danganta ne aka irin darussan daya koya a matsayinsa na mai zaman kansa ko lokacin da yayi zaman kan sa .

Ya lkasance darekta a wasu Kamfuna a nahiyoyi daban daban — Solcarbon SA-NƁ (Belgium), Ozbok Australia PTY Ltd, da kuma Belcarbon SA (Belgium) — ƙwarewar daya samu can  ne ta yasa ya ƙaru da wasu darussa ko ilmin da a halinyanzu yake amfanarsa  na nhaƙuri da juriya, riƙon amana da mfatan ci gaba koda yaushe.

Yanzu, shi babban jami’ai ne a Arbitrator at Silk Partners LLP (Nigeria), ya ci gaba da amfani da dokar shari’a ta kasuwanci,  da kuma sa Lauyoyi matasa masu tasowa su maida hankali domin watarana sune za su zama lauyoyi da kuma masu tsare- tsaren yadda za’ayi abubuwa.

Ƙudurin samar da zaman lafiya a Kudu maso gabas (PISE-P)

Abin ya wuce lamarin majalisa, bababar nasarar Kalu  abin ya shafi  hali ne, ba maganar majalisa ba.

Ta hanyar niyyarsa ta samar da zaman lafiya  a sashen Kudu maso gabas na Nijeriya wanda wata niyya ce ta ƙashin ƙansa (PISE-P), ya kira Shugabanni, masu Sarautun gargajiya, matasa, da kuma Shugabannin  inda aka zauna domin a gano inda matsalolin da suka sa haka suke da kuka yadda za a fuskance su  wajen maganin rashin tsaro a sashen Kudu maso gabas.

Babban saƙon ƙudurin na sa shi ne abu ne mai sauƙi, amma kuma idan ana maganar zaman lafiya: zaman lafiya ba hakan na nuna babu wata matsala ba a gaba, amma da akwai fahimtar juna.

Wannan tsarin na shi ya kasance wani abu ne da za ayi koyi da shi musamman ma, tsakanin al’ummomi inda zai yi wuya a rasa samun rashin jituwa tsakanin wannan wurin da kuma wancan wurin —saboda ai akan yi amfani da siyasa ne wajen maganin wata matsala ne ba ruruta wutar ƙiyayya ba. Ya yin da wasu suke gina bangaye shi ya gina a zauna domin tattauna zaman lafiya da yadda za’a ci gaba da yin sa

Ƙuduri da burin a taimakawa al’umma

Fiye da shera ashirin gidauniyar  Benjamin Kalu an yi amfani da ita wajen taimakawa mutane masu yawa a sassa daban- daban na Nijeriya, ta hanyar kula da lafiya , ilimi,  da  taimakawa mutane su samu tsaywa da ƙafafunsu,  kamnar mata ta hanyar tsare tsare  abin har ya kai ga zuwa ga matasa da kuma mutane n da ke da buƙata ta musamman.

Gidauniyarsa an yi amfani da ita ƙwarai inda ku,ma aka gane cewa shi lamarin wakilta dole ne ta kasance abin ba zai tsaya sai majalisar ba, don haka wasu al’umma suma suka samu dama har aka dama da su waɗanda suka tura Shugabnninsu  can.

Girmamawa da taimakawa al’umma

Ta hanyar nuna ana jin daɗin ayyukan da yayi ma ƙasa da kuma irin gudunmawar da ya bada ga ci gaban mulkin farar hula, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya ba shi nambar girmamawa ta  (CFR)  a shekarar  2024.

Amma babbar karramawar da aka yi ma Kalu, sau da yawa ya akan ce, “saboda yarda da amincewar al’ummar Bende ne.”  A shekara 54, ya zama wanda ake ta maganar shi ake ta yi , saboda irin taimakon da yake yiwa  al’ummar shi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL
Manyan Labarai

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI
Manyan Labarai

Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

October 25, 2025
Next Post
Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu

October 26, 2025
An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

October 25, 2025
An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

October 25, 2025

Daɓid Adeyemi

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.