A jiya ne, bayan da shugaban kasar Amurka Joseph Biden ya gama ziyararsa a yankin gabas ta tsakiya tare da komawa birnin Washington, manyan kafofin watsa labaru bi da bi suka bayyana ra’ayoyinsu kan wannan ziyara.
Kafin ziyarar, shugaba Biden ya taba bayyana cewa, za a bude sabon babi kan dangantakar dake tsakanin Amurka da yankin gabas ta tsakiya, amma ya koma ba tare da samun sakamako mai kyau ba.
Lokacin da Amurka ta fice daga kasar Afganistan cikin gaggawa ba tare da la’akari da muradun kawayenta ba, sannan kuma a lokacin da Amurka ta nuna bangaranci a fili kan batun Falasdinu da Isra’ila, kasashen yankin Gabas ta Tsakiya sun dade yanke kauna kan Amurka.
Haka kuma, a halin yanzu, kasashen yammacin duniya suna fuskantar matsalar hauhawar farashin kaya, yayin da kasashen yankin gabas ta tsakiya dake da albarkatun mai da iskar gas, suna da ‘yancin tsaida kuduri da kansu kan harkokin diplomasiyya, ba su son sauraron kasar Amurka.
A hakika, dalilin da ya haifar da wannan lamarin shi ne, yadda aka samu manyan sauye-sauye a tsarin duniya, da yadda ikon Amurka yake raguwa.
Tsarin da Biden ke da shi a yankin gabas ta tsakiya, ya shaida cewa, kasar Amurka ba ta da karfin tsaida kuduri kan batun yankin gabas ta tsakiya.
Wannan ba shi ne karo na farko ba, da manufofin diplomasiyya na kasar Amurka suka gamu da cikas, kana ba shi ne na karshe ba. (Zainab)