Yanzu haka, bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin (CIIE) karo na 8 yana gudana a birnin Shanghai na Sin. A wajen bikin, Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka samu matsayin Manyan Baki (Guests of Honor). Saboda haka, Najeriya ta tura wata babbar tawaga, a karkashin jagorancin shugaban majalisar wakilai ta kasar, Abbas Tajudeen, domin halartar bikin. Inda kuma ake shirin gudanar da wani taron tallata kayayyakin Najeriya na musamman.
A shafin yanar gizon bikin CIIE, an rubuta bayanin tallar Najeriya kamar haka: “Kamshin koko da na gyada, tamkar tsaraba ce daga kogin Kwara. Ruwan kogin na gudana ba tare da tsayawa ba, wanda ya taimaka wajen samar da dimbin amfanin gona. Najeriya, babbar bakuwa, na jiran ku a bikin CIIE karo na 8.” Bayanin nan ya nuna ni’imtaccen muhalli, da dimbin albarkatun noma na Najeriya.
Bikin CIIE shi ne bikin irinsa na farko da aka gudanar a duniya, wanda ya fi dora muhimmanci wajen baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su daga ketare. Kasar Sin ta kaddamar da bikin a shekarar 2018, da zummar aiwatar da manufarta ta bude kofa ga kasashen waje, da amfani da babbar kasuwarta ta cikin gida wajen samar da karin damammakin ci gaban tattalin arziki ga sauran kasashe.
An bude bikin CIIE na bana a ranar 5 ga watan Nuwamban da muke ciki, kuma za a ci gaba da gudanar da shi, har zuwa ranar 10 ga wata, inda aka samu kamfanoni 4108 na kasashen ketare da suke baje kolin kayayyakinsu. Duk a wannan biki, kasashe 17 na nahiyar Afirka sun kafa rumfunan baje kolin kayayyakinsu, kuma adadin kamfanoni masu baje kolin kaya daga nahiyar Afirka ya karu da kashi 80% , bisa adadin na shekarar bara.
Me ya sa bikin CIIE ke jan hankalin kamfanonin kasashen Afirka? Domin babbar kasuwar kasar Sin, da ta kunshi mutane biliyan 1.4, ta ba da damar sayar da karin kayayyaki, tare da samun riba mai tsoka. Misali, tun bayan da busasshen tattasan Ruwanda ya shiga kasuwannin kasar Sin, bisa damar bikin CIIE na shekarar 2021, noman tattasai ya riga ya zame wa ‘yan kasar wata muhimmiyar sana’a mai alaka da fitar da kayayyaki zuwa ketare, wadda ta ba dubun dubatar manoman kasar damar wadatar da kai. Bugu da kari, a bikin CIIE na shekarar 2024, wasu kayayyakin Afirka irin su zuman Zambia, da furanni na Kenya, da abarba na kasar Benin, su ma sun fara samun karbuwa tsakanin al’ummun kasar Sin.
Hassan Mohammed, jami’i mai kula da aikin kasuwanci a karamin ofishin jakadancin Najeriya dake birnin Shanghai na Sin, ya ce a bikin CIIE da ya gudana a bara, kamfanoni 13 daga cikin 16 na Najeriya sun yi nasarar kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa da abokan huldar kasar Sin, ciki har da wata kwangilar samar da tsabar koko, wadda kudinta ya kai sama da dalar Amurka miliyan 1.2. Bugu da kari, yazawa (kashu ko cashew) na Najeriya, da ba a san shi ba a baya a kasar Sin, yanzu yana kara samun karbuwa a kasar, duk albarkacin bikin CIIE.
Hausawa kan ce “Da abokin daka ake shan gari”. To, duk wadannan abubuwan da suka faru a bikin CIIE sun tabbatar da gaskiyar maganar. Ma iya cewa bikin ya nuna babbar ka’idar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wato samar da damammaki da amfanar da juna.
Sai dai, idan wani ya saba da neman sanin abubuwa game da kasar Sin ta hanyar rahotannin da kafofin watsa labaru na kasashen yamma suke bayarwa ko wallafawa, ba makawa zai cika da shakku da damuwa game da dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka. Saboda tunanin da Turawa ‘yan kasashen yamma suka saba da shi, ya shafi neman cin moriya da faduwar wani, da tattare samuwar dimbin albarkatu a hannun mutane kalilan, duk da cewa sauran mutane da yawa za su yi fama da talauci da yunwa.
Watakila wannan tunani nasu ya hana su fahimtar yanayin huldar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka na amfanin juna, da sanya su neman shafa kashin kaza ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka. Amma kamar yadda ake cewa “Gani Ya Kori Ji”, yadda kasar Sin ke kokarin taimakon kasashen Afirka wajen neman ci gaban tattalin arziki, zai rufe bakin gulmace-gulmacen masu yada jita-jita. (Bello Wang)














