Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau cewa, karuwar masu yawon bude ido na kasar Sin da na kasashen waje a lokacin bikin Bazara na shekarar dabbar Loong, ta sanya bikin Bazara ya zama kololuwar karuwar aikin yawon bude ido a duniya, da kuma baiwa duniya damar ganin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.
Alkaluma sun nuna cewa, a lokacin bikin Bazara, masu yawon bude ido na kasar Sin, sun kashe jimillar kudin da ya kai yuan biliyan 632.687, wanda ya karu da kashi 7.7 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar 2019, yawan kudaden da aka samu a fannin gidajen sinima na kasar Sin ya zarce yuan biliyan 8, lamarin da ya karya tarihi.
- Dambarwar Shari’ar Murja Kunya: Gwamnatin Kano Ta Musanta Yin Katsalandan Kan Shari’ar
- Wang Yi Ya Yi Tir Da Karairayin Da Ake Yi Game Da Xinjiang A Munich
Mao ta ce, kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga gudanar da mu’amalar mutane a tsakaninta da kasashen ketare, da ba da gudummawa ga kara bude kofa ga kasashen waje, da samar da yanayi mai kyau ga dukkan kasashen duniya, wajen raba damar da kasar Sin ke da ita.
Sannan game da batun ra’ayin jami’in kasar Philippines kan tsibirin Huangyan dake tekun kudancin Sin, Sin ta jaddada cewa, tsibirin Huangyan da yankunan tekun dake kewayensa mallakar kasar Sin ne.
Rahotanni na cewa, kakakin hukumar kula da kamun kifi da albarkatun ruwa ta kasar Philippines ya bayyana a ranar 17 ga wannan wata cewa, masunta na kasar Sin suna amfani da sinadarin cyanide a tsibirin Huangyan don lalata wuraren kamun kifi na kasar Philippines.
Game da wannan batu, Mao Ning ta bayyana cewa, lamarin da bangaren Philippines ya fada, ya kirkire shi ne da gangan. Gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan kiyaye muhallin halittu da tabbatar da albarkatun kifi, tare da dagewa wajen dakile kamun kifi ba bisa ka’ida ba.
Bugu da kari, game da Mao Ning ta gabatar da halartar ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a gun taron tsaro na Munich karo na 60, inda ta bayyana cewa, babban sakon da Wang Yi ya gabatar shi ne cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kiyaye manyan manufofinta na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ko da yaushe, a cikin duniya mai fama da tashin hankali
Mao Ning ta ce, kamata ya yi hadin gwiwa da samun nasara tare, su zama tushen manufofin dukkan kasashe wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa. Kasar Sin tana son hada kai da dukkan bangarori, don samun nasara tare, da kaucewa hasara da dama, da kara tabbatar da tabbas a duniya, da samar da makoma mai kyau ga daukacin bil-Adama. (Masu Fassarawa: IbrahimYaya, Zainab Zhang)