Bayan ayyana Bikin Bazara a matsayin ranar hutu na MDD, an kara samun abubuwa da dama dake nuna al’adun bikin a sassan duniya. An dauki Bikin Bazara na kasar Sin a matsayin bikin duniya, lamarin da zai sa kaimi ga jama’ar duniya su kara fahimtar kasar Sin da al’adunta tun daga wannan Bikin Bazara na Loong.
Bikin Bazara, bikin gargajiya ne mafi tsawon tarihi kuma mafi muhimmanci a kasar Sin. Shigar da bikin cikin ranekun hutu na MDD, ta shaida cewa, hukumomin MDD za su yi kokarin dakatar da gudanar da taruka a ranar Bikin Bazara ta ko wace shekara, don kara samar da dama ga jama’a su fahimci al’adun kasar Sin. A sakamakon hakan, an kara yada kasar Sin da al’adunta a fadin duniya.
Manazarta sun yi nuni da cewa, jama’ar duniya sun nuna amincewa ga ra’ayin hadin gwiwa tare da yin la’akari da bambance-bambance, da yin kokari tare don samun kyakkyawar makoma tare bisa tushen al’adun kasar Sin. Ta hanyar shiga bukukuwan murnar Bikin Bazara, jama’ar duniya suna kara fahimtar kasar Sin da ganin al’adun kasar Sin mai bude kofa da amincewa da bambance-bambance da yin kirkire-kirkire. Batun ya shaida cewa, Bikin Bazara ba na kasar Sin ne kadai ba, ya sa kaimi ga duk duniya wajen yin kokarin samun ci gaba tare. (Zainab Zhang)