A jiya ne, aka rufe bikin baje kolin cinikayyar ba da hidima na kasa da kasa na kasar Sin (CIFTIS) na shekarar 2023 a Beijing. A cikin kwanaki 5 da aka shafi aka gudanar da bikin, kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 83 sun kafa rumfunan nune-nune a bikin, mutane kusan 280,000 ne suka halarci bikin na bana, tare da cimma sakamako sama da 1,100, wannan ya shaida cewa, an nuna karfin zuciya kan tattalin arzikin Sin, hakan ya mayar da martani ga zargin da aka yi wa kasar Sin a fannin raguwar tattalin arziki.
Kasar Birtaniya, dake zama babbar bakuwa a bikin na CIFTIS a wannan karo, ta kafa tawaga mafi girma don halartar bikin a cikin shekaru 4, tare da kamfanoni da hukumomin kasar fiye da 60. Wakilin tawagar kasar Birtaniya ya bayyana cewa, bai amince da ra’ayin yanke huldar dake tsakanin Sin da sauran kasashe ba.
Kamfannonin Amurka su ma sun halarci bikin, inda kamfanonin Qualcomm da Intel suka kawo fasahohin zamani da dama. Idan aka tuna da labarin da aka bayar na cewa, shugabannin kamfanonin samar da mattarar bayanai ta microchip na kasar Amurka da dama sun ki amincewa da matakan gwamnatin kasar Amurka na kayyade fitar da mattarar bayanai ta microchip zuwa kasar Sin, hakika bikin CIFTIS na wannan karo ya aike da sakon kiyaye hulda a wannan fanni.
Wasu kafofin watsa labaru na kasashen waje sun yi bayani cewa, wasu mutane daga kasar Amurka da sauran kasashen yammacin duniya, sun zargi kasar Sin da samun raguwar tattalin arziki, saboda ba su samu kyakkyawar makoma a kasashensu a fannin kiyaye bunkasuwar tattalin arziki ba.
Suna fatan hankalinsu zai kwanta, idan suka ga Sin ta samu raguwar tattalin arziki. Amma wannan ba zai magance matsalolinsu ba. Ya kamata su nemi damar samun bunkasuwa da bikin CIFTIS na wannan karo ya samar. (Zainab)